Ba Sake Kama Tata Muka Yi Ba Gayyata Ce- DSP Gambo

  0
  810

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Katsina

  RUNDUNAR \’yan sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa ba ta sake kama Abdullahi Umar Tsauri ba wanda aka fi sani da Tata, gayyatarsa kawai suka yi domin ya amsa wasu tambayoyi saboda takardar koken da aka rubuta a kansa.

  Kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya shaida wa manema labarai DSP Isa Gambo ya ce an gayyace shi ne domin amsa tambayoyi.

  Kwanaki goma kenan da jami\’an tsaro suka kama shi kuma suka gabatar da shi a gaban kotun Majistare, lamarin da ya bayyana a kafofin sada zumunta cewa, an sake kama Tata, a garin Dutsi a kan shirinsa na rabon abincin Azumi ga marasa galihu.

  Gambo ya shaida wa manema labarai cewa takardar koken da wadansu jiga-jigan jihar suka sanya wa hannu kuma suka aika wa Gwamna Masari shi ne kwamishinan \’yan sandan ya gayyaci Tata.
  Mun gayyace shi ne domin ya yi mana bayani a kan koke guda shidda da aka yi a kansa domin barazana ce ga tsaro da kuma yin taro ba da izini ba.
  Kwamishinan \’yan sanda Usman Abdullahi ya gaya wa manema labarai cewa duk da yarjejeniyar da aka yi da Tata a rubuce amma sai Tata ya kasa girmama yarjejeniyar da yake cewa yaki da yunwa saboda lamarin zai iya haifar da tashin hankali da tunzura jama\’a.
  Amma a ta bakin Tata ya shaida wa manema labarai cewa ba su taka kowace doka ba domin shugabansu ya sanya wa wata takarda hannu don  a gaya wa \’yan sanda cewa za su kaddamar da gangamin yakin neman zabe a Dubai ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, 2017 kuma da karfe hudu na yamma.
  \”Muna tsammanin cewa takardar ta gamsar da duk wata maganar da kwamishinan ke bayani a kai.Kuma mun je wurin DPO a garin Dutsi muka rubuta wata takardar domin bayyana masa shirinmu na rufe yakin neman zabe inda muka shirya hawan daba domin kawata lamarin\”.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here