MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
JIYA Alhamis mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ya bukaci al’ummar kasar nan da su hada kansu ba tare da nuna wani bangaranci ko banbanci ba tsakanin su a mance da duk wani nuna son aware kana kuma a zauna lafiya domin zaman lafiya shi ne ke kawo ci gaban kasa da al’ummarta.
Mukaddashin ya bukaci haka ne a ziyarar kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnan Jihar Kuros Riba Sanata Ben.Ayade ya gayyace shi kaddamarwa a jawabin da ya yi a fadar sarkin Kalaba Obong Edidem Ekpo Okon Abasi Out V, lokacin da ya kai masa gaisuwar ban girma a fadarsa.
Haka nan kuma mai rikon kujerar shugabancin kasar Farfesa Osibanjo ya ci gaba da yin kira ga gwamnatoci da sarakunan gargajiya bisa alhakin da ya rataya a wuyansu na samar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin da suke mulka ko shugabanta.
A jawabinsa sarkin Kalaba wato Obong Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, ya bayyana takaicinsa na rashin sanya sarakunan gargajiya a farfajiyar tsarin mulkin kasa wanda a cewarsa su ne iyayen al’umma kuma su ne ya kamata a ba su kula a doka ta kasa wajen tarbiyyartar da al’umma .
Kafin ya baro fadar sai da sarkin Kalaba obong Ekpo okon ya ba shi sarautar gargajiya ta Adaidaha ke eburutu wato shugaba mai son zaman lafiya wadda sarauta ce ta kasaita ake bai wa fitattun mutane a al’adar Efik. Daga nan sai basaraken ya cira wa mukaddashin shugaban kasar hula na yaba masa da cewa shi ne shugaban da aka samu ya ziyarci fadarsa sauran da suka shude idan sun zo iyakacin su cikin gari su yi bukatar su su koma.