An Kama Wasu Manyan Mutane Uku A Saudiyya Da Kwayoyi

0
900

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A bayanan da suke fitowa daga kasar Saudiyya na cewa an kama wadansu mutane uku da aka samu kwayar da ake kira Tiramadol sama da dari uku a cikin kayan su.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa an samu wadannan mutanen ne sakamakon binciken da aka yi a cikin kayan su bayan da suka isa kasar Saudiyya domin yin aikin Umra.
Kamar dai yadda masu hannu da shuni suka saba aikatawa a duk lokacin da watan Azumi ya tsaya suna tafiya kasa mai tsarki domin yin aikin Umra.
A dokar kasar Saudiyya dai duk wanda aka samu da irin wannan keta dokar kisa ne babu wata tantama.
Shugaban hukumar Alhazai ta kasa, Barista Abdullahi Muktari Muhammad ya ce a bisa bayanan da aka samu daga wajen mutanen uku na nuni da cewa matsalar tamkar an saka masu wadannan kwayoyin ne.
\”Muna gargadin mahajjata aikin Hajji da masu zuwa Umra da su daina amincewa da kowa idan sun je filin jirgi ko filayen jirage domin tafiya wata kasa, ko da kuma kai babban mutum ne za a yi maka aiki na alfarma ya zama wajibi ka bi jakarka da fasfo dinka har ya zuwa ko ina sai an kammala komai\”.
Kamar yadda Barista Abdullahi Muktar ya bayyana cewa akwai alamun masu safarar kwayoyi ne suka bullo da wata hanyar saka wa jama\’a kwayoyi a cikin kayansu.don haka kowa ya kula babu batun ni babban mutum ne ko makamancin hakan.
Ana can dai ana gudanar da bincike a game da wadannan mutane da kayansu su uku inda kwayoyin suke a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here