Zuwa ga Edita
Bayan gaisuwa da fatar alheri, ina mai farin cikin sanar wa da masoyina kuma abin kwaikwayo a gare ni Dokta Bukar Usman cewa, dukan wallafe-wallafensa babu wanda zan ara ko a ba ni shi kyauta ban karu tare da fahimtar dimbin ilimin da yake a cikin kowane littafin nasa ba.
Ba abin da zan ce, sai Allah ya kara hazaka a wannan fage na adabi.
Ni ne naka
Falama Muhammad Bello