‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda A Bayelsa

0
814

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

WASU ‘yan bindiga sun harbe wani jami’in ‘yan sanda har lahira a ofishin ‘yan sanda na Sagbama,da ke karamar hukumar Sagbama ,jihar Bayelsa.’Yan ta’addan an ce su biyu ne suka zo a kan babur dauke da muggan makamai suka iske dan sandan a bakin aiki suka bude masa wuta daga nan su kuma suka kara gaba.

Wata majiya ta shaida wa wannan jarida cewa da misalin karfe 9 na dare ne dan sandan kaddarar ta fada masa, ya zuwa rubuta wannan labari ba a tantance sunan jami’in ba kana kuma makasan sun arce abinsu sai dai kuma rundunar ta sha alawashin farauto maharan tare da kama su a gurfanar da su gaban kuliya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa Asinim Butswat, ya shaida wa wakilinmu  aukuwar lamarin kana kuma ya ce jami’in nasu ba nan take ya mutu ba sai da aka kai shi asibiti,sannan ya sha alwashin rundunar za ta yi iyakacin bakin kokarinta ta gano makisan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here