Jihar Kebbi Ta Koma Ta Jam\’iyyar APC Baki Daya

  0
  1126
  Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna
  SAKAMAKON irin fitar kwarin dango da \’ya\’yan jam\’iyyar PDP suke yi a Jihar Kebbi suna shiga cikin APC ya sa wasu \’ya\’yan APC mai mulki a jihar suke kokawa da irin dimbin matsalolin da ka iya biyo baya musamman da korafin cewa suna yi ne domin bata APC a jihar.
  Wakilinmu na Kaduna ya bi diddigin yadda lamarin ficewa da komawa wata jam\’iyyar ya kasance ga kuma rahoton da ya kalato.
  Tsohon shugaban jam’iyar PDP, reshen Jihar Kebbi, Alhaji Bello Doya da kuma mutane 25,000 da suka hada da jiga-jigan jam’iyar ta PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyar APC a ranar Lahadi.
  Gwamna Atiku Bagudu, shugabannin jam’iyar APC, da kuma magoya bayan jam’iyar daga kananan hukumomin jihar 21 su ne suka karbi mutanen, cikin mutanen da suka sauya shekar har da Alhaji Isa Argungu,  tsohon Darakta Janar na yakin neman zaben Gwamna Sa’idu Dakingari, da kuma dan takarar jam’iyar PDP a zaben 2015, Sarkin Yaki Bello.
   Sauran wadanda suka sauya shekar sun hada da \’yan majalisar dokokin jiha masu ci su uku karkashin jagorancin Muhammad Isma’il, tsofaffin shugabannin kananan hukumomi goma,  da kuma shugabannin jam’iyar na kananan hukumomi da kuma mazabu.
   Shugaban jam’iyar APC na jihar,Attahiru Maccido, ya ce mutanen sun komo jam’iyar don kashin kansu.
  A nasa jawabin Gwamna Atiku Bagudu ya ce zai kula da su tamkar tsofaffin \’yan jam’iyar. Ya ce “APC rahama ce ga \’yan Najeriya, ta zamo jam’iyar kowa da kowa, a APC duk daya muke, za a  kula da kowa cikin mutunci da adalci,”
  Mai magana da yawun masu sauya shekar, Abdullahi Argungu, ya ce sun sauya shekar ne saboda irin ayyukan alherin da suke gani a matakin gwamnatin jiha da ta tarayya

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here