Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNATIN Jihar Kaduna ba za ta yi kasa a gwiwa ba har wasu su rika yin kalaman wargaza kasa ko haifar da hargitsi su yi tasiri a duk fadin jihar.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kaduna Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi a cibiyar \’yan jarida reshen Jihar Kaduna.
Aruwan ya ce tabbatancen al\’amari ne ga duk wanda ke kokarin haifar da batun bangaren ci ko kawo addini zai fuskanci hukunci kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
\”Gwamnati ta bayar da umarnin cewa a binciko tare da kamo dukkan masu wannan yunkurin da ya saba wa dokar kasa a duk inda suke a fadin jihar baki daya\”.
Kalaman nasu ba su yi wa gwamnatin jihar dadi ba, don haka kowa ya yi ta kansa tare da aiki domin ci gaban kasa da mutanenta gaba.
A ranar Talata ne matasan suka shaida wa manema labarai cewa sun gaji da gorace-gorace da gutsuri-tsoma daga kungiyoyin matasan kabilar Igbo masu neman kafa kasar Biafra a kudancin kasar nan.
Sai dai a wani taron manema labarai, mai magana da yawun Gwamna El-Rufai, Samuel Aruwan, ya yi tir da matakin nasu, yana mai cewa \”babu wani da zai hana wani zama a duk inda ya so kamar yadda tsarin mulki ya bada dama\”.
Ya kara da cewa gwamnati ta bayar da umarnin bincike da kamawa da kuma hukunta wadanda suka sa hannu kan sanarwar da matasan suka fitar.
\”Gwamnatin Kaduna ta dauki matakin ne saboda matasan sun yi wannan aika-aikar ne a jihar,\” a cewarsa.
Batun na kafa kasar Biafra dai na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al\’ummar kasar, musamman bayan bullar kungiyar matasan Igbo ta IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu.
Kwanan ne wata babbar kotu ta bayar da belin Mista Kanu bayan tsare shi bisa zargin cin amanar kasa.
Yana dai fafutikar ganin an gudanar da kuri\’ar raba-gardama ne kan batun kafa kasar ta Biafra.
Gwamnatin Kaduna ta ce idan wasu ba su gamsu da wasu abubuwa da ke faruwa a wasu jihohi ba, to bai kamata a maimaita irin wannan laifi ba, domin hakan ba shi ne mafita ba.
Ta kuma yi alkawarin kare hakkin duk wani dan Najeriya da ke zaune a jihar.