MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
KUNGIYAR da ke fafutukar hana cin zarafin ‘ya mace wadda a Turance ake kira da NETCUSA a taron da ta yi na da ta saba yi kowane bayan wata biyu a jiya Laraba ta zabi sababbin shugabannin da za su ja ragamar kungiyar na tsawon shekara da rabi .Zaben wanda aka gudanar a sakatariyar kungiyar masu nazarin hada magunguna da ke Kalaba an yi cikin lumana da kwanciyar hankali.
Wadanda aka zaba su ne Ukeme Ekong, mukamin shugaba yayin da Helen Kanu kuma sakatariya ,sai Eno Iyamba, matsayin jami’in hulda da jama’a na kungiyar . Shi kuma Musa Kutama,an zabe shi matsayin jami’in hulda da manema labarai na kungiyar.
Kungiyar network to curb sexual abuse wato netcusa kungiya ce wadda ba ta gwamnati ba muradin kungiyar kamar yadda jami’in hulda da ‘yan jarida na kungiyar ya sanar wa wakilinmu “kungiya ce wadda ba ta gwamnati ba kuma sadaukar da kai ake yi a aikin kungiyar da nufin kawo karshen cin zarafi da ake yi wa mata, kama tun daga fyade da kuma duka da sauran nau’i na gallazawa’ya mace”inji shi.
Nan ba da jimawa ba ne kungiyar za ta fara shiga lungu da sako na Kuros Riba domin wayar da kan jama’a membobin kungiyar sun hada da jami’an tsaro ma’aikatan kotu da kuma wasu da ke yi wa kungiyoyi da ba na gwamnati ba aiki ne a cikin netcusa.