Mustapha Imrana, Daga Kaduna
BARISTA Nasiruddeen Muhammad, kwamishinan ma\’aikatar kananan hukumomi da masarautun gargajiya ya bayyana kokarin da suka yi na sayo wa masarautun gargajiyar jihar dawakai da kayan adonsu da cewa abu ne mai kyau da zai inganta al\’amura a jihar.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wakilin BBC a Nijeriya.
Dawakan dai tare da kayan adonsu da kuma kayan wadanda za su hau dawakan an saye su kan kudi Naira miliyan 96 domin inganta gargajiya.
\”Irin goyon baya da hadin kai da masarautun ke ba gwamnati hakika sun cancanji a yi masu wannan domin harkar \’hawan sallah\’ da sarakunan ke yi wani bangare ne na yawan shakatawa wanda abu ne mai kyau\” inji Barista.
Sakamakon kashe wadannan kudi ya jawo ka-ce-na-ce a cikin jama\’ar jihar inda wasu ke cewa duk da matsalar da ake fama da ita na babu da rashin abinci amma sai ga gwamnati na kashe miliyan 96 domin sayen dawakan da sarakuna da wasu mutane za su hau.
Wani da ya zanta da Wakilinmu ta waya wanda dan asalin jihar Bauci ne ya bayyana lamarin da cewa tamkar gwamnatin da Barista ke yi wa shugabanci ba ta san abin da jama\’a ke ciki ba ne.