WANI DAN ACHABA YA ZAMA SANADIN AJALIN WANI MATASHI A GARIN ABUJA

0
906
Daga Usman Nasidi
WANI dan Achaba da ke tsananin manna gudu ya make wani dalibin ajin farko na jami’ar Abuja mai shekaru 22 a garin Gwagwalada, inda ya yi sanadiyyar ajalinsa kai tsaye, ba da jimawa ba.
Dalibin mai suna Ayatullah Galadima yana karantar ilimin fahimtar mu’amalar mutum ne a jami’ar Abuja, kuma ya gamu da ajalinsa ne da misalin karfe 3 na ranar Talata 6 ga watan Yuni.
Wani dan uwan mamacin mai suna Aliyu ya shaida wa majiyarmu cewar lamarin ya faru ne a titin Park a lokacin da mamacin ya fito daga banki, zai tsallaka titi.
“Akwai wani dan sanda a wajen da hatsarin ya faru, kuma shi ne ya garzaya da Galadima asibitin koyarwa na jami’ar Abuja, inda a nan ne ya riga mu gidan gaskiya.” Inji Aliyu.
Aliyu ya ce, tuni aka garzaya da gawar Galadima zuwa kauyen Rubochi inda aka yi masa jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar.
Shi ma shugaban sashin kula da harkokin dalibai na jami’ar, Dokta Peter Adakayi ya tabbatar da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here