Matsalar Tashin Bom: Mutum Biyu Sun Mutu Wasu Uku Sun Jikkata A Adamawa

0
1046

Muhammad Saleh, Daga Yola

TASHIN wani bom ya yi sanadiyyar mutuwar wasu yara biyu da jikkata wasu mutanen uku a garin Fadaman Rake da ke yankin karamar hukumar Hong a Jihar Adamawa.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Othman Abubakar, ya ce wasu mutane ne a cikin wata mota kirar Starlet, suka bai wa wasu yara biyu leda a kan su kai gidansu.

Ya ci gaba da cewa “Allah ya kiyaye ba su kai ga shiga gidan ba bom din ya tashi yaran biyu sun mutu wasu kuma sun jikkata, suna amsar magani a asibiti”. “Rashin sanin me ke cikin ledar ya sa yaran amsa suna kan hanyar tafiya da shi gida ne bom din ya fashe. “Yaran biyu sun mutu wasu mutanen uku hadi da wani mai wucewa sun jikkata an kai su asibiti a nan Hong” inji Abubakar.

Bording Kukuyaku wani mazaunin garin Hong, ya ce yaran suna wasa mutanen suka bai wa yaran da suke wasa a bakin hanya leda su kai gidansu.

Ya ce  “mutanen sun tsaya da motarsu kai ka ce taimako suke nema, sun bai wa daya daga cikin yaran da ke wasa a wajen leda cewa su kai gidansu, yaran ba su san ko mene ne a ciki ba sun dauka za su kai gida. “Yaran sun mutu nan take da tashin bom din, kuma wasu biyu sun ji mummunan rauni an kai su asibiti” inji Kukuyaku.     

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here