Amana Abar Tambaya Ce Gobe Kiyama – Ustaz M. M Mangu

0
1473

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

AN bayyana rashin amana da kuma kamanta gaskiya ce ta sanya tabarbarewar al’amura a Nijeriya da ma na zamantakewa musamman tsakanin shugabanni da wadanda ake shugabanta idan aka yi la’akari da hali mayuwaci da kowa yake kokawa da shi  a kasar nan.

Ustas Muhammad Salihu Musa Mangu ne ya bayyana wa dimbin al’ummar musulmin da suka halarci kasidar da ya gabatar jiya Lahadi a harabar masallacin kungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatis Sunnah ta kasa reshen jihar Kuros Riba da ke garin Kalaba a wa’azin da kwamitin matasa na kungiyar da ke Kalaba ya saba shiryawa kowace shekara tsakiyar watan Ramadan .

Taken kasidar na bana da malamin ya gabatar gaban dimbin musulmin da suka hallara a harabar masallacin suka saurara itace “gaskiya da rukon amana a musulunci”.A jawaban da yayi yayin karantar kasidar tasa malamin ya nuna illa tare da hadarin dake akwai wajen rashin amana da kuma kamanta gaskiya yaci gaba da cewa “rashin amana ne yake jawo tabarbarewar al,amura dana zamantakewa”.ya kara da cewa al,amura fa bazasu dai dai taba har sai al,ummar muslmi “mun tsaya mun rike amana mun kuma kamanta gaskiya kamar yadda koyarwar manzon Allah s.a.w. ya karantar da mu “.

Ustas Salihu Musa Mangu ya ci gaba da nuna halayyar wasu mutane musamman gasu musulmi da suke rike da madafun iko na gwamnati sukeyin yadda suka so da amanar da aka danka masu ta wannan ofishi da suke jagoranta ta yadda suke mayar da dukiyar gwamnati tamkar kayan gado suna yin yadda suka ga dama da ita idan an basu amanar aiki suki gudanar dashi yadda aka basushi nbis aamana a fi mayar da hankali wajen wawure kudin gwamnati ana barin talakawa ko oho “wajibi ne ,yan siyasa tun daga kan matakin kamsila shugaban karamar hukuma zuwa sama gwamna kake ko dan majalisar jiha ko ta tarayya ka sani cewa amana aka dan kamaka ta wannna ofishi da kuma ta talakawan da suka zabeka haka kuma jami,an tsaro tun daga kan ,yan sanda sojoji da kwastan da magirashin da ma sauran duk wasu masu sanya kayan sarki su sani amance ta rayuka da dukiyar jama,a aka danka ma su gobe kiyama Allah zai tambayesu.

Day a juya kan matasa na wannna zamani Ustan Muhammad Mangu ya nuna rashin jin dadinda da irin yadda matasan yanzu suka mayar da kwaikwayon aski ko sanya tufafi irin nay an wasan kwallo ko kuma mawaka kana kuma a su karankansu basu siffantuwa da wata siffa irin ta kamala ko ta mutanen kirki kuma wasu daga ciki saboda irin rashin aman na wasu matasan ne suke kasancewa ana barin su a baya suna shiga bangar siyasa da sauran shaye-shayen kayan maye da aiyyuka na ta,addanci don haka “ina kira ga matasa su kasanc emasu amana a duk wasu harkoki da matasan suka tsinci kansu”.Karshe ya jawo hankalin jami,an tsaro ,yan jaridu sakatarori yan siyasa da duk wasun masu rike da madafun iko das u sani fa amana ce aka danka masu gwamnatoci da shugabannin ma haka domin ranar gobe kiyama za,a tambaye su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here