Musulunci Cike Yake Da Kyawawan Halaye –Ustaz M.B. Adam

0
1673

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

AN bayyana cewa tarbiyya da horaswa na da matukar muhimmanci a Musulunci domin tana koyar mana da yadda za a zauna da juna lafiya har ma da wadanda ba musulmin ba ma su yi sha’awar addinin su shigo musamman ganin yadda tarbiyya ta Musulunci ta kasance abin a gani a yi koyi da ita ne kamar yadda tun zamanin Manzo ka gani daga gare shi na kyawawan halaye da kuma dabi’u masu kyau haka kuma ya koya wa sahabbansa da sauran al’ummar musulmi wanda har ila hazar yanzu muke koyi da shi.

Ustas Muhammad Bashir Adam , ne ya fadi haka yayin gabatar da wata kasida mai taken “muhimmancin tarbiyya da horas wa a Musulunci”wanda kwamitin wa’azin matasa na JIBWIS da ke Kalaba ya gudanar a harabar masallacin .

Ya ce Musulunci ya karantar  da al’ummar musulmi yadda za su zauna lafiya da junanan su da kuma sauran jama’a wadanda ba musulmin ba ne da ma sauran masu bin addinin gargajiya haka nan kuma addini ne na tausayi da kuma taimaka wa masu karamin karfi ya bada misalin “wata rana Manzon Allah s.a.w. ya ga wata tsohuwa ta daure itace tana son ta dauka amma babu wani kusa da zai zo ya dora mata a kai ta tafi sai Allah Ya kawo Annabi ya ganta maimakon da ya dauki itacen ya dora mata inji malamin sai shi da dauka ya wuce gaba tsohuwar tana binsa har gidanta. Bayan da suka isa gidan tsohuwa sai Annabi ya ajiye mata itace suka yi ban kwana har ya tafi sai tsohuwar ta kira shi ya dawo ta ce ya ga yana da halaye nagari amma za ta ba shi shawara akwai wani mutum na nan mai suna Muhammadu yana raba mutane da addinin su kada ka shiga addinsa. Nan take sai fiyayyen halitta ya ce ai ni ne Muhammadu ita kuma ta tambaye shi irin addinin nasa karshe nan take dai wannan tsohuwa ita ma ta karbi Musulunci saboda me saboda ta ga tarbiyya da halaye nagari na Manzon Allah kuma ta san lallai addinin ba na wasa ba ne”injishi.

Ustas Bashir Adam, ya kara da cewa “saboda tarbiya bda horaswa tagari da addinin musulunci yayi mana ne ma ya sanya mana yafiya da kuma yi wa juna afuwa”.Sai dai malamin ya ragargaji mutanen da ba su da adalci tsakanin iyalansu da kuma abokan zaman su yace masu hali irin wannan ba karantarwa ce ta Manzon tsira ba shi addinin Musulunci addini ne da ya yi horo kodayaushe da halaye nagari.

Bayan da aka kammala wa,azin wakilinmu ya tambayi malamin ko wane irin buri ake son cimma w aga matasan sai yace “su kasance masu tsoron Allah kamanta gaskiya da kuma rike amana kana kuma su rungumi sana’a ban da zaman kashe wando ana bukatar matashi duk inda yake ya zama mai kazar-kazar wajen neman ilmi da kuma halaliyarsa kamar yadda na zo na ga matasan muslmi na Kalaba suna yi haka ake bukata sauran matasa musulmi da ke sassan Nijeriya da ma duniya baki daya su kasance masu kuzari wajen neman sani da kuma halaliyar su”.injishi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here