Sun Yi Ram Da Wani Kasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane

0
1094

Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna

RUNDUNAR \’yan sandan Nijeriya ta sanar da kame wani shahararren mai garkuwa da mutane mai suna Chukudi a garin Legas.
\’Yan sandan sun sanar da cewa sun kama shi ne tare da wadansu mutane shida bayan yin musayar wuta da mutanensa.
An kuma kama wani mai suna Evans a cikin wani kasaitaccen gidansa na alfarma a wata unguwa a Legas kuma yana taimaka wa jami an tsaro wajen gudanar da bincike.
Shi dai Chukudi ya tara dimbin dukiyar da ta kai Tiriliyoyin Naira ta hanyar garkuwa da mutane a ciki da wajen Nijeriya.
Kayan da aka gano a wurinsu sun hada da bindigogi kirar AK 47 da masu sarrafa kansu, albarusai da sauran dimbin miyagun makamai da suke amfani da su wajen gudanar da aikinsu na sata tare da garkuwa da mutane.
Kuma jami\’an tsaron na \’yan sandan a Legas sun bayyana cewa Evans na taimakonsu domin gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here