Zubairu A Sada, Daga Abuja
DOMIN amincewa da shiri tare da yunkurin Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Hajiya A\’isha Muhammadu Buhari na ciyar da rayukan mata da yara kanana gaba a fadin kasar nan, musamman ma \’yan Arewa maso Gabashi da suka fuskanci bala\’o\’i da dama, kasar Sin wato Caina ta tallafa wa shirin da kudi har Naira Miliyan sittin.
A lokacin da take karbar tallafin a madadin Uwargida A\’isha Buhari, Babbar mataimakiya ta musamman ta shugaban kasa, Dokta Hajo Sani da ta wakilce ta, ta ce wajibi ne su nuna farin cikinsu da wannan tallafi da kasar Sin ta yi wa shirin na uwargidan shugaban kasa. Kuma ta ba da tabbacin cewa, tallafin zai kai ga wadanda aka yi shi domin su.
Dokta Hajo Sani ta ci gaba da bayyana yunkurin uwargidan shugaban kasa na tattara kudade domin tallafa wa mutane \’yan gudun hijira a Najeriya da wadanda bala\’i ya auka masu a dukan fadin Afrika ta yamma. Ta ce wannan tallafi na kasar Sin zai kai har kasashen na Afrika.
Da yake mika tallafin, Ambasada Lin Jin ya ce, sun lura da shirin na uwargidan shugaban kasa ya taimaka ainun a fannin kiwon lafiya da rayuwar mata da yara da masu rauni kwarai, sannan shirin ya ci nasarar manufarsa na dawo da rayuwar ire-iren wadannan \’yan Adam bisa mizani mai annashuwa. Ya ce wannan ne ya sanya suka kalli zumuncin nan da idon rahama don a agaza wa mutane, kuma shirin na uwargidan ya kai ga ko ina da ina.