Daga Usman Nasidi
DAGA wurare daban-daban a mazabar Kogi ta yamma, mazauna na ci gaba da kokarin cire Sanatansu, Sanata Dino Melaye.
Melaye yana zargin cewa Gwamnan jihar Yahaya Bello na kashe Biliyoyin Naira domin yi masa zagon kasa
Duk da cewa magoya bayan Sanata Dino Melaye da ke mazabar Kabba/Bunnu a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuni sun lashi takobin ba za a tsige dan majalisar ba, har yanzu ana ci gaba da zaben tsige shi a mazabarsa.
Game da cewar rahotanni, mazauna Odo Ape a Kabba/Bunu daga Egba a karamar hukumar Yagba suna jere cikin layi yau Talata, 13 ga watan Yuni domin rattaba hannayensu kan takardan tsige shi.
Magoya bayan Melaye a ranar Lahadi sun sha alwashin cewa lallai sai sun tsige shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Mathew Ojo Kolawole wanda suke zargi da zagon kasa tsige Melaye.