DAWO DA ALKALAN DA AKE ZARGI DA CIN HANCI RUSHE SHARI\’A NE A NIJERIYA-FARFESA DADARI

0
724
  Isah Ahmed, Jos
WANI malami a sashen binciken aikin gona da koyar da dabarun noma na Jami\’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Salihu Adamu Dadari ya bayyana cewa matakin da hukumar kula da kotunan Nijeriya ta dauka, na dawo da alkalan nan guda 5 da ake zargi da cin hanci da rashawa da aka kama a kwanakin baya,kan aikinsu rushe shari\’a ne a Nijeriya.
Farfesa Salihu Adamu Dadari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce wannan mataki da wannan hukuma ta  dauka yana nuna cewa alkalanci ya rushe a Nijeriya.  Domin ba  a binciki zargin da ake yi wa wadannan alKalai da aka kama kamar yadda ya kamata ba. Ya ce  an sami wadannan alkalai  da daloli na fitar hankali, amma yanzu an wanke su an ce wadannan kudade nasu ne.
Ya ce wannan ya nuna cewa tsarin shari\’ar Nijeriya tun daga sama har kasa a lalace yake.
\’\’Idan aka lura ko kwamitin bincike aka kafa kan wadanda suka sace kudaden gwamnati.Idan aka kai wa Alkalan Nijeriya sai su yi watanda da shari\’ar. A rika jan kafa da shari\’ar  har a dauki tsawon lokaci ba tare da an yanke hukumci kan wannan shari\’a ba. Misali akwai tsofaffin  gwamnoni da aka kama  da laifin aikata  almundahana a lokacin da suke kan mulki a jihohinsu, akwai wanda shari\’arsa ta fi shekara 10 har yanzu ba a yanke ba. Kuma a yanzu wannan tsohon gwamna yana majalisar dattawa ana tsara dokokin kasar nan da shi.Irin miyagun abubuwan da shugaban kasa Muhammad Buhari yake kokari yaka kenan a Nijeriya\’\’.
Farfesa Dadari ya yi bayanin cewa ba  wannan hukumar ce ya kamata tanada wadanda za su binciki wadannan alkalai ba. Ya ce ya kamata gwamnati ta kafa wani kwamitin alkalai masu zaman kansu don su binciki wadannan alkalai da ake zargi da cin hanci. Wanda aka samu da laifi a hukumta shi, wanda kuma ba a samu  da laifi ba a sake shi. Farfesa Dadari ya yi kira ga alkalan Nijeriya su hada kansu su rika hukunta duk wanda ya yi laifi a Nijeriya. Domin  idan babu shari\’a za a ci gaba da  samun  masu kashe mutane da masu sata da sauran miyagun laifuffuka a Nijeriya.
  •  

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here