GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA HANA HAWA BABURA A WASU SASSAN JIHAR

0
783
Daga Usman Nasidi
GWAMNATIN jihar Kaduna ta bada umarnin hana hawa babura a wasu sassan garuruwan inda ake fama da matsalar garkuwa da mutane a yankunan.
Mai bai wa Gwamnan jihar shawara a kan harkokin tsaro, Kanal Yusuf Yakubu Soja ne ya bayyana hakan inda ya ce majalisar tsaro ta jihar ta haramta hawa babur a wasu garuruwa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin a samu sukunin yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa.
Babban jami\’in da ke kula da ayyukan yaki da miyagun ayyuka wato (Operation Yaki), ya kara da cewa sun dauki matakin ne bayan tattaunawa a majalisar tsaro ta jihar wadda ta samu halarcin sarakuna da kuma hakiman yankin da abin ya shafa.
Ya ce dokar za ta fara aiki ne daga garin Kakau zuwa Jere wadanda suke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A cewarsa, Babban Sufeton \’yan sandan kasar ya aika da jami\’an \’yan sanda 600 wadanda za su rika yin sintiri a kan babbar hanyar don farauto masu garkuwa da mutane.
Hakazalika, wani wanda yake sana\’ar acaba a garin Jere Iliyasu Umar, ya cewa a gaskiya ba su ji dadin daukar wannan matakin ba domin da wannan sana\’ar suke ci, suke sha, to idan babu wannan sana\’ar za su koma gida su zauna kenan?
Ya ci gaba da cewa \”yan acaba ba su da hannu a satar mutane don haka bai kamata a hana mu yin acaba ba.\”
Jihar Kaduna dai a halin yanzu na daya daga cikin jihohin arewacin kasar da suke fama da matsalar satar mutane musamman a wadannan yankunan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here