KOWA YA JE YA YI KATIN ZAMA DAN KASA – Inji El-Rufa\’i

0
812
Daga Usman Nasidi
GWAMNATIN Jihar Kaduna ta sanar da fara yin rijistar ga duk wani mazaunin jihar domin sanin iya adadin mutanen da ke zama a cikinta.
Kwamishinan kasafin kudin Jihar, Mohammed Abdullahi ne ya sanar da haka ranar Laraba da yake nasa rijistan a Kaduna.
Mohammed ya ce gwamnati ta fitar da haka ne saboda ta san iya adadin mutanen da ke zama a karkashinta sannan kuma ta iya wadata al’umman da ababen more rayuwa.
Gwamnati ta umurci duk wani wanda zai zauna a jihar da zai kai kwanaki 180 da ya tabbata ya yi wannan rijista.
Ya ce: “wasu daga cikin dalilan yin wannan rajista shi ne domin gwamnati ta iya samar wa mutane ababen more rayuwa da kuma kara samar da tsaro a jihar.”
Ya kara da cewa gwamnati na shirin samar wa mutanen jihar ababen more rayuwa wanda sai mutum yana da wannan shaida ne za a iya amfana da wasu daga cikin su.
Ya ce mutane su ziyarci wuraren da gwamnati ta kirkiro domin yin rajistan ko kuma a je ma’aikatar samar da da katin shaidar zama dan kasa domin a yi rajista.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here