SIYASA AKIDA TA YI ALLAH WADAI DA WA\’ADIN DA AKA DEBAR WA INYAMURAI SU BAR AREWA

    0
    793
    Isah Ahmed, Jos
    A ci gaba da dambarwar da ke gudana a Nijeriya kan wa\’adin da wata kungiyar matasar arewa ta debar wa \’yan kabilar inyamurai su bar jihohin arewa nan da watanni uku. Kungiyar yakin neman zaven shugaban kasa mai zuwa na shekara ta 2019 na tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, mai suna Siyasa Akida ta yi Allah wadai da wannan furuci da kungiya ta yi.
    Kungiyar ta Siyasa Akida ta yi Allah wadai da wannan furuci ne, a wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Aliyu Tukur Gansta ya raba wa \’yan jarida.
    Sanarwar ta ce furuci da kungiyar ta yi zai iya kawo damuwa a Nijeriya, domin ya saba da ginin da shugabannin kasar nan na farko suka yi, kan zaman lafiya da kaunar juna da hadin kan al\’ummar kasar nan.
    Sanarwar ta yi bayanin cewa akwai yarinta da rashin hujjoji kan  wannan furuci da wannan kungiya ta yi. Domin ba daidai ba ne a nuna wa dukkan wata kabila banbanci ko wariya a kasar nan ba. Don haka sanarwar ta yi kira ga al\’ummar Nijeriya su hada kansu su zauna lafiya su yi watsi da irin wadannan furuce-furace, wadanda za su iya kawo  damuwa a Nijeriya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here