WANI MUTUM YA HALLAKA MATARSA SABODA BA TA WANKE MASA KAYA BA

0
830
Daga Usman Nasidi
WANI mutumin Jihar Benuwe mai suna Mathew ya hallaka matarsa, abar kaunarsa, uwar \’ya\’yansa uku, mai suna Hannah saboda wani abu da bai kai ya kawo ba, ko a ce, abin da bai taka kara ya karya ba.
Su dai wadannan matasa sun dade suna tare, amma a ranar da lamarin ya auku, Hannah wanda take dauke da ciki wata 8 ta ci duka a hannun Mathew a gidansu da ke Abuja, sakamakon kin wanke masa kayansa da suka baci.
Rahotanni sun bayyana cewa dalilin da ya hana Hannah wanke kayan Mathew kuwa shi ne, a ranar ta wuni a asibiti inda ta je awo, ko da ta dawo, yamma ta yi, don haka sai ta dage yin wankin sai washegari. Da gogan naka ya dawo sai ya dinga fada, ita kuwa tana ba shi hakuri.
Daga nan ne fa ya dirar mata, ya shiga dukanta, ya yi mata lilis har sai da ya hallaka ta. Sai dai makwabtansu sun bada shaidar cewa Mathew ya dade yana cutar da Hannah saboda ba ta haifa masa da namiji ba.
Wata makwabciyarsu, Uwargida Joy ta bada shaida a kan Hannah, inda ta ce “Hannah ta yi kokari matuka wajen kulawa da \’ya\’yanta mata su uku, don har aikatau take yi a wata makaranta ba tare da sanin Mathew ba don ta samu abin ciyar da \’ya\’yanta.”
Daga karshe dai matan unguwar sun gudanar da zanga-zanga inda suka kai karar Mathew ofishin \’yan sanda, kuma tuni an kama shi, an daure shi yayin da ake gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here