Mustapha Imrana Abdullahi Kaduna
SAKAMAKON wani kakkarfan zargi da ya yi tsanani, majalisar dokokin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin da zai binciki zargin da suke yi wa shugabansu na karbar kudi daga hamshakin dan kasuwa Dakta Aliko Dangote a kokarinsa na ganin ya hana \’yan majalisar cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi daga sarautar.
Su dai \’yan majalisar sun zargi shugabansu da yin mirsisi a kan kudin tun bayan da ya karbi cin hancin miliyan dari daga dan kasuwar amma ya ki daunawa da kowa a cikinsu.
Zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano ya yamutse sakamakon zargin rashin adalci da ‘ya’yan majalisar ke yi wa kakakin majalisar, Rayit Honarabul Kabiru Rurum wajen rabon Naira miliyan 100 da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Ali Dongote ya bai wa ‘yan majalisar don su dakatar da binciken da suke yi a kan Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi Lamido bisa zarge-zargen kashe kudaden masarautar Kano ba bisa ka’ida ba da kuma wasu laifuka 7.
Jaridar DAILY NIGERIANS ta rawaito daga majiya mai tushe cewa, Alhaji Aliko Dangote ya bai wa ‘yan majalisar Kano wuri na gugan wuri Naira miliyan 100 don su janye binciken da suke yi a kan San Kano wanda ake zargi da yin facaka da kudaden masarautar Kano da adadinsu ya kai Naira Biliyan 4. Ganin cewa ci gaba da binciken ka iya sanya Sarkin ya rasa kujerarsa, ya sa Dangote da wasu manyan kasar nan suka shiga cikin maganar don tsare wa Sarki Muhammadu sanusi II mulkinsa.
Idan ba mu manta ba dai a ranar 10 ga watan Mayu ne majalisar ta Jihar Kano ta kafa wani kwamiti na mutum bakwai don su gudanar da bincikensu a kan zargin da ake yi wa Sarkin Kano bisa wasu laifuka har guda 8.
Sai dai kuma a ranar 22 ga watan Mayun, sai majalisar ta bayyana janye ko kuma dakatar da wannan bincike bisa roko da Gwamnan Jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi a wata takarda da ya rubata wa majalisar, inda a cikinta ya bayyana cewa ya samu kira daga mutane daban-daban na ya dakatar da binciken da ke ci gaba da faruwa a kan Sarkin Kano.
Cikin mutanen da Gwamnan na Kano ya ambata a matsayin wadanda suke so lalle a dakatar da wannan bincike sun hada da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Aliko Dangote, Janar Ibrahim Babangida, Janar Abdussalami Abubakar, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da dai sauran manyan kasar nan.
Wani daga cikin ‘yan majalisar ta Jihar Kano da ya bukaci da kar a bayyana sunansa ya ce, bisa rabon Naira Miliyan 100 da Dangote ya ba su bai masa dadi ba. Ya shaida wa jaridar DAILY NIGERIANS cewa lalle babu shakka Aliko Dangote ya ba su Naira Milyan 100 don su dakatar da binciken, amma sai kakakin majalisar, Kabiru Rurum ya yi sama da fadi da kudin shi kadai.
“Jim kadan bayan mun kafa kwamitin da zai binciki Sarkin Kano sai Dangote ya ba mu Naira Miliyan 100 don mu dakata ta hannun kakakin majalisa”
“Amma sai kakakin majalisa ya yi shiru ya ki fada wa kowa. Don mun dauka ma bai karbi kudin ba har sai da asirinsa ya tonu a ‘yan kwanakin nan”.
Haka kuma dan majalisar ya bayyana cewa kakakin majalisar Jihar Kano ya karbi kudade daga wajen wasu wadanda suke son a sauke Sarkin. Zuwa yanzu dai ‘yan majalisar sun kafa wani kwamitin bincike a kan kakakin majalisar
Daily Nigerian ta tuntubi mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote amma sai ya ce yana halartar wani taro ne a yanzu, saboda haka babu abin da zai iya cewa.
Sai dai kuma hukumar yaki da zamba da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta ci gaba da gudanar da bincikenta a boye a kan Sarkin Kano tun ranar da majalisa ta bayyana dakatar da nata binciken.
“Mun yi nisa wajen gudanar da wancan bincike kan Sarkin Kano kuma da zarar mun hattama za mu mika sakamakon binciken ga Gwamnan Kano”, in ji wani ma’aikacin hukumar da ya bukaci da a sakaya sunansa.