Yadda Aka Yi Na Shafe Shekaru 32 A Gidan Yari -Ibrahim Karaye

0
891

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba.

WANI direba da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a kurkuku,  ya  shafe shekara 32. Tsare mai suna Ibrahim Muhammad Karaye, wanda haifaffen garin Karaye ta Jihar Kano ne ya kasance yana gudanar da harkokinsa na tukin mota  a birnin Legas tun a shekarun baya kuma a shekara ta 1985 ne kaddara ta fada masa inda a cikin rashin sani ya dauki fasinja da suka yi shatarsa zuwa wani gida ashe barayi ne ‘yan fashi da makami suka je fashi wani gida da ke Unguwar Ibebite bayan ya sauke fasinjansa, ashe wasu mutane da ke saman bene sun dauki lambar motarsa bai sani ba lamarin da karshe ya zame masa jangwam aka zo har gida aka kama shi a wancan lokaci.

Ibrahim Karaye ya yi wa wakilinmu na kudanci a Kalaba  bayani yadda lamarin ya faru har ma yadda aka tsare shi da hukuncin da kotu ta yanke masa na daurin rai da rai ko mene ne musabbain da aka kai shi jarun “Ni direba ne laifina cikin rashin sani na dauki ‘yan fashi na kai wata unguwa mai suna Ibebite da ke Legas , na ajiye su na dawo to ni ban san cewa mutanen da na dauka ba ‘yan fashi da makami ne na dauke su a Aguda ,Surulere na sauke su a layin Ibebite,  na koma lokacin da ina komawa wasu mutane a saman bene ashe sun dauki lambar mota ta ashe fasinjan da na sauke da daddare sun je sun yi fashi da safe aka kama mutum 2 daga cikin su dama su 5 ne na dauka na sauke su a wurin sauran 3 sun gudu sai aka kai su ofishin ‘yan sanda da aka tambaye su wa ya kawo su sai suka ce wani direba ne misalin karfe takwas na dare, an tambayi ‘yan fashin sun san direba suka ce a’a sai mutanen can suka ba da lambar motata ga ‘yan sanda sai ‘yan sanda suka dauki mota guda 4.,cike da ‘yan sanda  suka je suka zagaye gidan da muke tun da sun ga mota ta a waje.”injishi.

Ya ci gaba da bayani “Daga nan  suka  ce ina mai motar nan na ce ga ni nan suka ce an kama ni, na ce masu ai ban san abin da na yi ba suka ce idan ka je ofis ka yi bayani. A can da muka je ofishinsu aka tambaye ni ko na san wadancan mutane na ce masu a’a ni ban san ko daya daga ciki ba, na san dai sun tsayar da ni na dauke su a mota zan kai su Ibebite na dauke su na tafi. Suka sake tambayata ko tare muka je sata? Na ce masu a’a suka ce su biyar ne suka je sata an kama biyu uku daga cikin su sun gudu amma an kama mai dafa abinci da maigadi na gidan mun zama mu biyar ke nan da aka kama aka kai mu Ikeja wajen kwamishina. Ofisa mai kula da masu laifin da ake zargi wato O.C ya ware mu mu uku ya ce wadancan ba barayi ba ne aka tababtar da biyun ‘yan fashi ne daga nan mai gabatar da kara a ofishin ‘yan sanda na Aguda ya ba su kudi ya ce a kaimu Panti a kai mu kotu. Bayan da aka kai mu kotu alkali ya saurari jawabinmu sai ya ce min shi ba zai iya sanyawa a sake mu ba sai a zarge shi da cin hanci daga nan alkali ya yanke min hukuncin daurin rai-da -rai   su kuma aka harbe ‘yan fashin”.

Muhammad Karaye ya ci gaba da cewa “ na shafe shekara talatin da biyu a kurkuku. A kurkuku na Ikoyi na fara zama aka mayar da ni Kirikiri, daga nan aka mayar da ni na Benin aka sake dawo da ni kurkukun Fatakwal a shekara ta 2001aka mayar da ni Akwa Ibom Uyo daga can ma a 2004 aka dawo da ni nan Kalaba, shi ne Allah Ya kawo karshen zaman  ina daya daga cikin wadanda Gwamnan Jihar Kuros Riba Sanata Farfesa Ben. Ayade ya yi wa afuwa.

Ko akwai wani darasi da ka koya zaman ka na jarun sai ya ce “hakika na koyi yadda zan zauna da mutane da kuma kowane irin mutum sannna na koyi sana’ar birkila da kuma ta yin fenti ina cikin koyon sana’ar dinki ne Gwamna ya yi mana afuwa”. An tambaye shi ko zai iya gane gida? Ya ci gaba da cewa zai iya ganewa amma fa idan ya tambaya, kana kuma wadanda suka mutu sun mutu wadanda kuma suke raye suna raye a gana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here