AL\’UMMAR FILATO SUN AMFANA DA SHIRIN TALLAFIN BUHARI-SUMAYE

    0
    935
    Isah Ahmed, Jos
    DOKTA  Sumaye Hamza ita ce shugabar shirin tallafa wa jama\’a na shugaban kasa a jihar Filato. A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu, ta bayyana cewa babu shakka al\’ummar jihar Filato sun amfana da wannan shiri. Domin ya zuwa yanzu wannan shiri ya dauki matasa 3375  aiki, tare da bai wa mata da dama rancen kudade don su ja jari.
    Ga yadda tattaunawa ta kasance:-
    GTK: Ya zuwa yanzu wanne hali ake ciki dangane da ayyukan wannnan shiri a Jihar Filato?
    Dokta Sumaye Hamza: To ya zuwa yanzu ayyuka kan wannan shiri na tallafa wa jama\’a yana tafiya daidai a Jihar Filato. Misali kamar a bangaren tallafa wa matasan da suka kammala karatun jami\’a, wadanda ba su da aikin yi, mun dauki matasa 3375 a kashin farko. Kuma wadannan matasa suna nan suna aiki, a cikin wadannan matasa kadan ne ba a fara biyansu albashi ba. Amma yawancinsu an fara biyansu albashi, yanzu ma sun karbi na wajen watanni 6.
    Wasu har sun fara aikin gona da irin kudaden da ake ba su, wasu sun fara kiwo da kudaden da aka ba su, wasu sun kama sana\’o\’in abin wuya da \’yan kunne, wasu sun shiga ayyukan taimaka wa jama\’a da kudaden da aka ba su. Wannan ya nuna mana cewa lallai wannan tallafi ya yi masu amfani, tare da sauran mutane da suke tare da su.
    Wadanda kuma suka zabi su koyi sana\’o\’i nan ba da dadewa ba, za a tura su wuraren da za a koya masu sana\’o\’in.
    Kuma a ranar 13 ga watan da ya gabata an fara  tura takardun neman shiga wannan shiri kashi na biyu, ta yanar gizo a ko\’ina a fadin kasar nan.
    GTK: Duk da wannan bayani da kike yi, wasu suna cewa har yanzu ba su ga ayyukan wannan shiri ba,  a nan Jihar Filato?
    Dokta Sumaye Hamza: A tawa fahimtar masu fadin irin wadannan maganganu wadanda ba sa bukatar a taimaka wa mabukata ne. Domin yanzu a kasar nan, duk wanda aka tambaya kan shirin N-Power zai tabbatar maka da cewa  ya san da shirin. Maganar dafa abincin yara \’yan makaranta shi ma yana nan za a fara gudanar da shi, nan bada dadewa ba.  Maganar tallafin kudi na naira dubu biyar-biyar shi ma mun yi nisa da shi, nan bada
    dadewa ba za a fara bayar da wadannan kudade, a kananan hukumomi 6 na jihar nan da za a fara da su. Kuma an bai wa kungiyoyin matan jihar nan rance kudade a dukkan kananan hukumomin jihar nan guda 17 don su ja jari.
    GTK: A takaice wanne irin amfani ne kike ganin cewa al\’ummar Jihar Filato sun yi da wannan shiri na tallafa wa al\’umma?
    Dokta Sumaye Hamza: Akwai amfani da dama da al\’ummar Jihar Filato suka samu a kan wannan shiri na tallafa wa al\’umma. Na farko dai a dauke maka nauyin matasa 3375 a ba su ayyukan yi. Wadanda ada basa komai suna zaune a gida, wannan babban amfani ne da aka samu.
    Bayan haka mata da dama da suke cikin kungiyoyi wadanda aka ba su tallafi don su kara jari don yin kiwo ko noma shi ma wannan wani babban amfani ne da al\’ummar Jihar Filato suka samu a wannan shiri.
    Sannan kuma akwai maganar bai wa yara abinci, wanda nan ba da dadewa ba, za a fara a nan Jihar Filato. A wannan shiri na bai wa yaran makaranta abinci mutane da dama za su sami abin yi, kamar masu dafa abincin da dai sauransu.
    Bayan wannan kuma ga maganar tallafin kudi na naira dubu biyar-biyar shi ma nan bada dadewa ba za a fara.
    GTK: Duk da wadannan ayyuka da kuke yi, a \’yan kwanakin nan hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da rahoton cewa rashin aikin yi ya karu a Nijeriya, mene ne za ki ce kan wannan al\’marai?
    Dokta Sumaye Hamza: Abin da ya sa gwamnatin tarayya ta fito da wannan shiri na tallafa wa jama\’a shi ne a cikin ma\’aikatan gwamnati, akwai ma\’aikatan da suka yi ritaya saboda lokacinsu ya cika. Akwai  wadanda suka rasu akwai wadanda suka bar aikin saboda wasu dalilai.
    Bayan haka kuma gwamnati ta yi la\’akari da wadanda suka gama makarantun gaba da sakandire da ba su da aikin yi. Saboda haka ta kirkiro wannan shiri, don a tallafa wa irin wadannan mutane su sami abin yi. Babu shakka idan wannan shiri ya ci gaba za a magance rashin aikin yi a Nijeriya.
    GTK: A ganinki wadanne hanyoyi ne kike ganin za a bi a magance rashin aikin yi a Nijeriya?
    Dokta Sumaye Hamza: Hanyoyin da za a bi a magance rashin aikin yi a Nijeriya shi ne a rika fadakar da jama\’a cewa ba sai sun jira gwamnati ta ba su aikin yi ba. Kuma  akwai abubuwa da yawa wadanda jama\’a za su iya yi, su da kansu misali kamar aikin noma da kiwo wadanda za mu iya yi ba tare da mun jira gwamnati, don ta ba mu aikin yi ba. Domin noma shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar nan. Don haka babu shakka idan muka rungumi noma za a warware matsalar rashin aikin yi a Nijeriya.
    GTK: To, wane sako ko kira ne kike da shi zuwa ga al\’ummar Jihar Filato dangane da ayyukan wannan shiri na tallafa wa al\’umma?
    Dokta Sumaye Hamza: Kira na ga al\’ummar Jihar Filato dangane da ayyukan wannan shiri, shi ne duk lokacin da aka ce ga wani abu ya fito kan wannan shiri su fito su nemi a ba su wannan abin. Domin idan ba mu yi haka ba, sai dai muj i ana bai wa wasu  wannan tallafi a wasu jihohi.
    Don haka mu tashi mu rika bin wannan shiri sau da kafa, domin mu ma mu amfana kamar yadda kowa yake amfana a Nijeriya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here