WATA BAKATSINIYA TA YI WA WANI MATASHI KACIYA BAYAN YA YI MATA FYADE

0
1019
Daga Usman Nasidi
WANI lamari mai ban ta’ajibi ya wakana a wata kotun Jihar Katsina inda aka gurfanar da wani kato mai shekaru 30 sakamakon yarinyar da ake zargi ya yi wa fyade ta yanke masa al’aura.
Kakakin rundunar \’yan sandan Jihar Katsina, DSP Isa Gambo ne ya shaida wa manema cewa an kama mutumin ne a lokacin da ya je neman samun shaidu daga wajen \’yan sanda, a matsayin sharadin da likita ya gindaya masa kafin ya duba shi.
Kakakin ya ce \’yan sanda sun gano hakan ne yayin da suka yi masa \’yan tambayoyi kan yadda ya ji raunin, inda daga bisani suka fahimci ya jiyo raunin ne sa’ailin da yake yi wa wata yarinyar fyade.
Wannan mummunan lamari, kamar yadda majiyarmu ta ruwaito, ya faru ne a garin Kankara a ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata.
Daga karshe Alkalin kotun, mai shari’a Fadile Dikko ya bada umarnin a tasa keyar mutumin zuwa gidan kurkuku, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here