MUNA DA BURIN MASALLACIN SULTAN BELLO YA ZAMA CIBIYAR HADA KAN MUSULMIN NIJERIYA-SHEIKH SULAIMAN

    0
    736
    Isah Ahmed, Jos
    SHEIKH  Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman shi ne  babban Limamin masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, kuma malami a tsangayar koyar da ilmin addinin Musulunci da ke jami\’ar Jihar Kaduna. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya yi dogon bayani kan irin shirye-shiryen da suke na bunkasa wannan masallaci, wanda marigayi Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello ya gina. Don ganin masallacin ya zama wata babbar cibiya ta yada ilmi da hada kan musulmin al\’ummar Nijeriya.
    Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
    GTK: A matsayinka na babban limamin masallacin Sultan Bello da ke Kaduna wanne kokari kuke yi, na ganin an bunkasa wannan masallaci?
    Sheikh Sulaiman: Wato shi dai masallacin Sultan Bello,  masallaci ne mai tarihi. Domin marigayi Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ne suka yi kokarin assasa shi.
    A bangaren gyara ruhi da tarbiya wato bangaren addini, marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ne ya tsaya a wannan masallaci. A yayin da a bangaren mulki kuma marigayi Sa Ahmadu Bello ne ya taimaka wa wannan masallaci.
    Don haka muna tunanin mu ga cewa wannan masallaci yana karbar kowanne mai mulki idan ya zo masallacin, ya tabbatar hankalinsa a kwance  babu wanda zai ci masa mutumci, babu wanda zai wulakanta shi. Saboda wannan masallaci mulki ne ya kafa shi.
    Haka nan kuma tarbiyya da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya kafa, ya zamanto ita ce ake aiwatar da ita a wannan masallaci.
    Ka ga dukkan bangarorin nan guda biyu suna da matukar muhimmanci  a wannan masallaci, domin kowanne yana bada gudunmawarsa. Bangaren masu mulki su taimaka a gyara masallacin, bangaren masu ilmin addinin Musulunci  kuma su gyara zukatan mutane.
    Babu shakka wannan masallaci yana bukatar gyare-gyare,  don haka  a yanzu ana nan ana  kan wadannan gyare-gyare domin a inganta shi. Ta yadda duk wanda ya zo sallah zai yi sallah a cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
    Ya zuwa yanzu dukkan fitilun masallacin an gyara su, bayin Allah sun taimaka wasu sun bayar da kudade, wasu sun bayar da kayayyakin aiki.
    Bayan haka wuraren da masallacin yake yoyon ruwa, akwai wani bawan Allah da ya dauki nauyin gyara wannan yoyon ruwa. Wato aikin da wannan bawan Allah yake daukar nauyin yi,  a wannan masallaci ko sabon ginin masallacin za a yi, sai haka.
    Kuma muna son mu sanya Screen a wannan masallaci saboda yana da girma, domin a kalla masallacin yana daukar masallata sama da mutum dubu 7 da dari biyar. Saboda haka idan liman yana karatu ko yana huduba, wadanda suke nesa ba sa hango shi.  Don haka muna son mu sanya Screen a wannan masallaci. Ta yadda dukkan abin da ake yi a cikin masallacin mutum zai iya gani a duk inda ya zauna, a wajen masallacin.
    Kuma tuni mun riga mun tsara taswirar gina makarantar koyar da aikin jinya da asibiti, a wannan masallaci. Ka ga idan muka gina wannan asibiti zai taimaka wa al\’ummar da suke makwabtaka da wannan masallaci.
    Abu na gaba muna son mu samar wa wannan masallaci wakafi, wato duk kudin da masallacin ya samu za a saka su a ciki don gudanar da harkokin masallacin. Masu gadin wannan masallaci da ma\’aikatan masallacin in Allah ya yarda, za mu dinka masu yunifom wanda in mutum ya gan su zai san cewa ma\’aikatan masallacin ne.
    A bangaren ilimi mun  bude bangarori daban-daban na koyar da karatun Alkura\’ani mai girma guda 19. Akwai bangaren manya da yara da mata da wadanda suke koyon hada baki da wadanda sun iya hada bakin da wadanda suke son yin hadda da alaramomi wadanda suke son a gyara masu harufan da suke futarwa wajen karatun Alkura\’anin  da wadanda sun haddace Alkura\’anin suna son a ba su shedar cewa sun haddace shi da dai
    sauransu.
    Kuma ana yin darusan karatun addinin Musulunci a wannan masallaci, a
    duk tsawon mako.
    GTK: Mene ne babban burinku a wannan masallaci?
    Sheikh Sulaiman: Babban burinmu  shi ne wannan masallaci ya zamanto cibiyar yada ilimi da tarbiyar al\’umma  da koyar da dabi\’u nagari. Kuma burinmu ne wannan masallaci ya zamanto cibiya ta taimakon al\’umma da sasanta al\’umma da hada kan al\’ummar musulmin Nijeriya da duniya baki daya.
    GTK: Idan muka koma ga bangaren dambarwar da ake ta yi kan kudin aikin hajjin bana, a matsayinka na wanda ya dade yana taimaka wa alhazai a lokacin aikin hajji mene ne za ka ce kan wannan al\’amari?
    Sheikh Sulaiman: Harka ta karyewar dajarar kudadenmu da aka samu a kasar nan, ita ce ta kawo wannan matsala.Domin idan mutum ya lura zai ga ba aikin hajji ne, kadai abubuwa suka tsawwala  ba. Duk wani abu na rayuwa babu abin da farashinsa  bai tashi ba.
    A shekarun baya ina iya tunawa a shekara ta 1994 kudaden guzurin  da aka bai wa  alhazai,  da suka canza sai suka ga sun haura kudin kujerar da suka bayar, wato sun ci riba kan abin da suka biya. Amma yanzu saboda wannan matsala ta karyewar darajar kudinmu, a kullum abin yana karuwa.
    Wannan abin kuma ya shafi duniya ne baki daya, domin a kwanakin baya na je Umara na ga yadda kayayyaki suka tashi a Saudiyya. Abin da ka sa  kana saye kan Riyal daya a da, yanzu ana sayar da shi Riyal uku.
    A takaice abin da nake son na ce aikin hajji abu ne na wanda Allah Yake ba da iko. Idan mutum ya ga ba shi da iko kada ya takura wa kansa. Sai mutum ya yi wasu ibadun, Allah Ya dauke masa nauyin. Saboda haka ni a wurina gaskiya tashin farashin kayayyaki ne  ya kawo wannan matsala. Domin duk mutumin da yake Nijeriya ya san cewa kayayyaki sun tashi. Saboda haka mutane su saukaka wa kansu, zage-zage ba zai fitar da mu daga cikin wannan matsala ba.
    A maimakon haka a roki gwamnati ta cire wani bangare na wasu nauye-nauye na aikin hajjin. Tun da wadannan alhazai \’yan kasa ne domin ana yi wa \’yan kwallo ma irin wannan tallafi. Don haka tun da alhazan nan za su je su yi wa kasa addu\’ne ya kamata a taimaka a rage masu kudin wannan kujera ta aikin hajji. Domin babu abin da al\’ummar kasar nan
    suke amfana da shi, a cikin dukiyar kasar nan, sai ta irin wadannan hanyoyi. Don haka gwamnati ta saukaka wa alhazan kasar nan kan  wannan kudin kujera da aka fada.
    GTK: A \’yan kwanakin nan an sami damuwa kan wa\’adin  da wasu matasan Arewa suka debar wa al\’ummar Ibo su bar arewa, a matsayinku na malaman addini yaya kuke kallon wannan al\’amari?
    Sheikh Sulaiman: To wannan magana ce wadda ta shafi siyasa. Su wadancan abokan zama namu ya kamata su sani cewa Allah Madaukakin Sarki ne Ya hada mu zauna tare. Da Allah bai so ba, da tuni suna kasarsu mu ma muna tamu kasar. Ya kamata su fahimci cewa su ba za su iya wadata da barinmu ba, haka mu ma ba za mu iya ba.
    Don haka maimakon su yi ta tada hayaniya suna kira ta yadda za a zo har a zubar da jini. Ya kamata su bi abin a hankali, kamar yadda kudunacin kasar Sudan suka yi,  a raba kasar nan ba tare da an zubar da jini ba.
    Suna da \’yancin su ce suna son kasarsu, su je su rike kasarsu mu ma arewa za mu rike kasarmu. Amma dai mu sani cewa haduwarmu mu dunkule waje guda, zai fi alheri a gare mu baki daya.
    Su kuma matasanmu su sani cewa suna da shugabanni suna da iyaye kuma sarakuna da malamai da dattijan kasa duk sun yi bayani, matasan sun janye daga wannan ra\’ayi nasu. Amma duk da haka ina kira ga matasa idan irin wannan al\’amari ya taso kada su yanke hukunci, domin yanke hukunci ga matashi babu alheri a cikinsa. Domin ba zai iya hango abin da iyayensa da malamansa suke hangowa ba.
    GTK: To, a karshe wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al\’ummar Nijeriya?
    Sheikh Sulaiman: Kira na ga al\’ummar Nijeriya shi ne mu sani cewa a kowace kasa Allah Yana hada ta da irin mutanen da suke zaune a wannan kasa. Kuma kowane mutum da yake zaune a kowace kasa yana da gudunmawar da zai iya bayarwa. Muna da abubuwa da dama da muke taimaka wa Inyamurai,  su ma suna da abubuwa da dama da suke taimaka
    mana. Amma dai idan an rabu din wani bangare zai fi wani bangare shan wahala.
    Mu dai na  tabbatar a matsayinmu na wadanda muka fi yawa kuma musulmai, mun san Allah ne yake azurtawa kuma Shi ne yake yin komai, don haka za mu iya rayuwa a kowane irin hali. Saboda haka idan matasan Inyamurai suna yin irin wadannan abubuwa iyayensu da shugabanninsu su ja masu kunne.  Kuma gwamnati kada ta zuba ido tana ganin kowa yana fadar irin abin da ransa yake so. Kuma ina kira ga malamai da fastoci su rika yin wa\’azi ga jama\’a suna fadakar da su kan illolin tayar da fitina.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here