Gwamnati Ta Ba Da Ranakun Litinin Da Talata Hutun Salla Karama

0
771

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNATIN tarayyar Nijeriya ta bayar da sanarwa cewa ranar Litinin da ta yi daidai da 26 ga watan Yuni da kuma Talata 27 ga watan a matsayin ranakun hutun karamar sallah.

Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Bello Dambazau ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ya bukaci musulmi da sauran \’yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin hutun domin yi wa kasa addu\’ar zaman lafiya tare da kaunar juna.

Dambazau ya kuma yi kira ga \’yan Nijeriya da su guji batutuwan da za su kawo tsana a tsakanin junansu kuma a hada hannu da gwamnatin Muhammadu Buhari domin gina ingantacciyar kasar da kowa zai yi alfahari da ita

Ya kuma jaddada aniyar gwamnati na kare lafiya da dukiyar \’yan kasa,ya kuma kara tabbatar wa da jama\’ a cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba na ganin an yi maganin wani ko gungun jama\’ar da za su yi kokarin tayar da zaune-tsaye.

Minista Dambazau ya kara jaddada kudirin gwamnati wajen yi wa kowa adalci, gwamnati na yi wa kowa murnar zaman lafiya tare da yin bukukuwan sallah lami lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here