KUNGIYAR IZALA ZA TA BUDE MAKARANTUN KOYAR DA SANA\’O\’IN HANNU

    0
    1001
    Isah Ahmed, Jos
    KUNGIYAR Jama\’atu Izalatil Bid\’ah Wa\’ikamatis Sunnah ta kasa za ta bude
    makarantun koyar da sana\’o\’in hannu a kowanne lungu da sako na kasar
    nan. Shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Sheikh Muhammad
    Sani Yahya Jingir ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen
    rufe  taron kara wa juna sani na watan Azumin Ramadan, da kwamitin
    wa\’azin matasa na kasa na kungiyar ya shirya a garin Jos.
    Ya ce tuni kungiyar ta kafa wani  kwamiti don gudanar da wannan aiki
    na bude makarantun koyar da sana\’o\’in hannu a ko\’ina a cikin kasar nan.
    Ya ce  da yardar  Allah  nan  ba da dadewa ba za mu rika koyawa matasa
    da mata sana\’o\’i daban daban, a wadannan makarantu da za mu bude.
    \’\’Kungiyar ta dauki wannan mataki na bude irin wadannan makarantu ne
    domin ba da gudunmawarta wajen ganin an samar wa matasan kasar nan da
    ayyukan yi\’\’.
    Ya yi kira ga  matasa kan su guji shan miyagun kwayoyi su zamanto masu tarbiyya.
    Daga nan ya yaba wa kwamitin wa\’azin matasa na kungiyar kan irin ayyukan da suke gudanarwa.
    A nasa jawabin mai martaba Sarkin Kanam Alhaji Mu\’azu Muhammad Babangida ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan su dauki masu sana\’o\’in hannu su basu aikin koya wa matasa sana\’o\’i daban-daban. Ya ce daukar irin wannan mataki zai kawo karshen matsalar rashin aikin yi a Nijeriya.
    Ya ce  nan gaba samar wa al\’ummar kasar nan  aikin gwamnati zai yi wuya, saboda yawan al\’ummar da suke karuwa a kullum, don haka daukar wannan mataki ya zama wajibi.
    Tun da farko a nasa jawabin shugaban kwamitin wa\’azin matasa na kasa na kungiyar Ustaz Muhammad Murtala Idris Malwa ya bayyana cewa wannan taron kara wa juna sani da suka shirya, suna gudanar da shi ne a kowanne watan Azumin Ramadan don ilmintar da matasa.
    Ya ce a cikin wannan wata na Azumin  bana, sun je babban gidan yarin Jos, sun tallafa wa fursunoni da buhunan  shinkafa  15 da  buhun suga 2 da buhunan gero  6 da buhunan kayayyakin sawa.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here