Shugaba Buhari Ya Rubuto Wasikar Ta\’aziyyar Danmasanin Kano Daga Ingila

0
794

Mustapha Imrana Da Zubair Sada, Daga Kaduna

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya rubuto wasikar ta\’aziyyar rasuwar Danmasanin Kano, Alhaji Dokta Maitama Sule ga Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje daga can kasar Ingila.

Shugaban wanda da hannunsa ya rubuto wasikar kuma ya sanya mata sa hannunsa, ya ce yana yi wa gwamnatin Jihar Kano ta\’aziyyar rasuwar Maitama, inda ya kara da cewa, ba sai an fadi ba rasuwarsa gibi ne babba da cike shi yake da wahalar gaske a jihar da ma kasar Najeriya baki daya.

Maitama Sule Danmasanin Kano dai ya rasu ne a wani asibitin da ke kasar Kairo (cairo).

Maitama Sule ya taba zama minista a Jamhuriya ta farko kuma ya zama Jakadan Nijeriya a majalisar Dinkin Duniya, kuma a yanzu jagora ne a kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum. Ana sa ran za a taho da gawarsa daga Misra zuwa Kano a yau Talata in Allah ya nufa domin yi masa sutura da jana\’iza. Allah ya gafarta masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here