GWAMNATI TA KARA SANYA IDO KAN SHAN KAYAYYAKIN MAYE A NIJERIYA-USTAZ ALIYU ALIYU  

0
662
 Isah Ahmed, Jos
 
BABBAN limamin masallacin juma’a na ‘yan doya da ke cikin garin Jos babban birnin jihar Filato Ustaz Aliyu Aliyu Muhammad ya yi kira ga hukumomin Nijeriya kan su kara sanya ido kan yaki da shan kayayyakin maye a Nijeriya. Ustaz Aliyu Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa.
 
Ya ce yin wannan kira ya zama wajibi ganin yadda wannan al’amari ya zama babban barazana a kasar nan. Ya ce a yau matasan kasar nan,  sun mayar da abubuwan sanya maye kamar wani abinci.
‘’Wadannan kayayyakin sanya maye suna da matukar illoli domin suna illanta yara, su mayar da su marasa kishin kansu, su koma sai dai a basu  komai.  Wadannan kayayyakin sanya maye sukan sanya fada  tsakanin matasa, har su  kai ga  kisan kai a junansu.  Sannan  kuma masu shan irin wadannan miyagun kayayyakin maye dabi’unsu sukan koma kamar na mata’’.
 
Ustaz Aliyu Aliyu ya yi bayanin cewa abin mamaki gwamnati tana da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa [NDLEA]. Amma idan mutum ya shiga garuruwa da kauyukan kasar nan, zai ga yadda ake sayar da wadannan miyagun kayayyakin sanya maye ana sayarwa a ko’ina.  Wannan babban abin bakin ciki ne.
Ya ce don haka lallai ne hukuma ta sanya ido kan ma’aikatan wannan hukuma a debi ma’aikata masu tsoran Allah, domin su rika gudanar da wannan aiki.
 
Har’ila yau ya yi kira ga jama’a  su rika  kafa kungiyoyi a garuruwa da unguwanni domin su rika zakulo irin  mutanen da  suke sayar da irin wadannan  miyagun kayayyakin sanya maye.  Ya ce ya kamata  iyayen yara su rika bada goyon baya, ta hanyar na tona asirin irin mutanen da suke sayar da irin wadannan  kayayyakin sanya maye. Duk wanda aka san yana sayar da irin wadannan kayayyaki a sanar da jami’an tsaro. Kuma a daina bai wa irin wadannan mutane hayar gidaje da shaguna.
 
Daga nan ya yi kira ga masu irin wannan sana’a su ji tsoran Allah domin duk lokacin da ka cutar da dan wani ta hanyar sayar masa da miyagun kayayyakin maye, kada mutum ya yi tsammanin dukiyar da ya tara ta wannan hanya zata yi albarka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here