Isah Ahmed, Jos
SAKATAREN jam’iyyar APC na jihar Filato Alhaji Bashir Musa Sati ya bayyana cewa nan bada dadewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Filato. Alhaji Bashir Musa Sati ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce alkawarin da gwamnan jihar ta Filato Simon Lalong ya yi na zaben kananan hukumomi a jihar ya yi nisa, domin tuni gwamnan ya yi gyare gyare kan dokokin hukumar zaben jihar, ya nada mata shugaba da sakatare da sauran mambobi. Kuma ya kaiwa majalisar dokokin jihar, majalisa ta duba wannan gyara ta amince, an mikawa hukumar zaben nan. Ita kuma ta mikawa ma’aikatar shari’a idan suka gama dubawa zasu mikawa gwamna.
Har’ila yau yace a ‘yan kwanakin nan gwamnan ya rushe shugabannin riko na qananan hukumomin jihar. Duk wadannan abubuwa suna nuna cewa za a yi zaben kananan hukumomi nan bada dadewa ba a jihar.
‘’Don haka muna kira ga Jama’ar jihar Filato su kara hakuri nan gaba kadan, za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar nan. Kuma za a yi zabe mai kyau mai inganci wanda babu magudi a cikinsa’’.
Alhaji Musa Sati ya yi bayanin cewa a bangaren jam’iyyasu ta APC a shirye suke don gudanar da wannan zabe. Kuma da yardar Allah sune zasu lashe wannan zabe, domin basu da wata damuwa.
Ya ce jam’iyyar PDP da take adawa da su, ba zata sake yin wani tasiri ba a jihar Filato, domin tayi mulkinta na shekara 16 a jihar ta gama.
Ya ce gwamnatin APC a jihar Filato tana tafiyar gaskiya da tsafta babu rudu babu yaudara a jihar.