Daga Usman Nasidi
MAI alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa dangane da yadda kafafen sadarwa na zamani ke kawar da hankulan yara mata a kasar nan.
Sarkin ya nuna wannan damuwa tasa ne a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli ya yi rufe gasan Al-kur’ani na kasa da ya gudana a Jihar Sakkwato, inda ya ce: “Abin damuwa ne yadda shafukan sadarwa ke dauke hankulan \’ya\’yanmu daga karatuttukansu.
Ya ce “Kafafen sadarwa irin su Facebook, Whatsapp, Twitter, 2go da Intagram na dauke hankulan \’ya\’yanmu.
Matsalar ta fi shafar \’yan matanmu, musamman yadda su ne iyayen al’umma, wanda idan suka gyaru kowa ya gyaru.” Inji Sarkin.
Sarkin yana shawartar iyaye da su dage wajen ganin \’ya\’yansu sun yi haddar Kur’ani, tare da jan kunnen musulmai da su guji duk wani hali da ka iya kawo ci baya ga sunan addinin su.
A karshen taron, wadda ta zo ta daya a gasar, Husna Nura daga Jihar Katsina ta samu kyautar Naira dubu 100,000 daga wajen Sarkin Muslmi Sa’ad, sa’annan shi ma Gwamnan jihar ya bata kyautan Naira dubu 150,000, kujerar Makkah da na’aurar samar da kankara.
Yayin da sauran mahaddatan da suka fafata a gasar suka samu kyautar Naira dubu 10,000 duk mutum daya daga wajen Sarkin.