Ambaliyar Ruwa Ya Kashe Mutum Shida A Suleja

0
772

Rabo Haladu Daga Kaduna

AKALLA mutum shida ne suka mutu bayan saukar wani ruwan sama a garin Suleja na Jihar Neja , kamar yadda wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa, ruwan saman ya jawo ambaliya da rushewar gidaje da kuma gadoji a unguwannin hanyar Kaduna Road na yankin karamar hukumar Suleja mai makwabtaka da birnin Abuja.
\”An fara ruwan saman ne tun daren Asabar da misalin karfe 11 na dare har zuwa wayewar gari . Daga nan ne sai ambaliyar ruwan ta fara gadan-gadan a unguwar Hayin Nasarawa,\” in ji Dahiru Adamu, wani mazaunin wurin da al\’amarin ya faru.
Ya ci gaba da cewa \”Ruwan ya ci motoci da gidaje da dama, kuma akalla mutum shida sun rigaya sun mutu. Kuma mun yi asarar dukiya mai yawa daga wannan amabaliyar ruwan.\”
Kokarin jin ta bakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ya ci tura don ba su amsa kiran da muka yi musu ta waya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here