Daga Usman Nasidi
YANZU haka dai al\’amurra sun fara dagulewa a can jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya inda wasu matasa suka daura damarar lallai sai sun maido shugaban majalisar dattijai gida.
Matasan dai da dattijai \’yan asalin mazabar Bukola Saraki din ne wadanda suka taru suka kafa wata kungiya mai suna \’Dole ne jihar Kwara ta canja\’ wato \’Kwara Must Change\’ a turance.
Majiyarmu ta tsinkayi shugaban wannan kungiya mai suna Abdulrazaq O Hamzat yana mai cewa yana ba dukkan daukacin \’yan Najeriya hakuri game da zaben tumun daren da suka yi.
Amma a cewarsa, sun yi da-na-sanin yin hakan su kansu kuma yanzu haka sun daura damarar ganin ya dawo gida kamar yadda ake shirin yi wa babban yaronsa a majalisar wato Sanata Dino Melaye.