Daga Usman Nasidi
DARURUWAN jama’a daga mazaɓar Ƙiru da Bebeji sun fara gangamin yi wa dan majalisar su Abdulmuminu Jibrin kiranye daga majalisar wakilai ta tarayya.
Wannan taro ya gudana ne a garin Dakatsalle, inda shugaban gangamin Alhaji Salele Bushasha ya bayyana cewar sun kudirci yi wa Jibrin kiranye ne saboda rashin girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Abdulmuminu Kofa baya nuna damuwa ga al’ummarsa, kuma baya girmama shugabannin majalisar wakilai, don haka ne muka tattara dukkanin bayanan da suka dace don yi masa kiranye, za mu fara wannan yunkuri a ranar 30 ga watan Yuli”
Abdulmuminu Jibrin Bushasha ya kara da cewa tun da dai Jibrin ya yi watsi da su, toh zai gani a kwaryarsa, don haka za su dawo da shi gida, inji majiyarmu.
Cikin wadanda suka halarci gangamin akwai shugaban kungiyar matasa reshen karamar hukumar Bebeji, Abdulrashid Isah, shugaban kungiyar malamai, NUT reshen Bebeji, Yusuf Garba da sauran \’yan siyasa daga manyan jam’iyyun adawa da APC.