Ana Sayar Da Takin Buhari Dubu 7,200 A Funtuwa

0
804

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

KASUWAR Funtuwa dai wuri ne da ake samun tururuwar baki da yawa daga wurare daban daban a ciki da wajen Nijeriya musamman ga kamfanoni da sauran dukkan mi son sayen kayan amfanin gona.
Kuma wani abin farin ciki shi ne gwamnatin Jihar Katsina ta samu damar kafa kamfanin da ake harhada takin zamani a cikin garin Funtuwa a wurin da ake cewa Holo kusa da muhimman wurare biyu wato tashar jirgin kasa da kuma unguwar Tudun Wada.
Amma a kasuwar wannan babban birnin da ke sama wa gwamnatin Katsina da ta tarayya makudan kudi kuma yake sama wa dimbin manema da wadataccen takin zamani Sai ga shi lamarin ya zama wani al\’amari daban.
Domin kuwa a garin da ake hada wannan takin zamani mai suna Tak Agro 20 -10 – 10 da ake cewa takin Buhari mai albarka saboda nagarta takin wanda a dalilin hakan ya sa a yanzu takin zamani ya zamanto wa manoma da sauka da duk dan kasa nagari da manoma ke alfahari da shi.
Kamar yadda kowa ya sani gwamnatin tarayya karkashin Buhari ta bayyana farashin takin da ta kawo a kan kudi Naira dubu biyar da dari biyar a ko\’ina a duk fadin kasar.
Amma sai ga shi a halin yanzu muna samun dimbin matsalolin mummunan karin farashin takin, har ma a wannan gari na Funtuwa inda ake sayar da takin a halin yanzu a kan kudi Naira dubu bakwai da dari biyu a garin da kamfanin yake wanda hakan ya saba wa abin da Muhammadu Buhari ya shirya wa kasar baki daya.
Kamar yadda muka zagaya kasuwar Funtuwa da kuma ji daga bakin \’yan kasuwa da sauran jama\’a, wani dan kasuwa da ya kasance babban dilan takin da kuma sauran kayan noma ya shaida mana cewa shi tun da ba a shirya sayar masu da takin ba shi ya kama wata sana\’ar daban.
Bangaren manoma kuma ba su ji dadin irin yadda ake sayar da takin a garin Funtuwa to tambayar manoman ita ce nawa za a sayar a wadansu jihohin da garuruwan?
Za mu ci gaba da kawo maku irin bincike da tattaunawar da muka yi a kan wannan al\’amari na takin Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here