Daga Usman Nasidi
WANI mamakon ruwan sama da aka samu mai karfin gaske a karamar hukumar Kaita da ke a jihar Katsina ya yi mummunar barna a karshen satin da ya gabata kamar yadda rahotanninmu suke nuni.
Kamfanin jaridar Vanguard dai ya ruwaito cewa kimanin gidaje sama da 100 ne suka rushe sannan kuma munane sama da 2000 suka rasa matsuguni a karamar hukumar inda al\’amarin ya faru.
Majiyarmu ta samu labarin kuma cewa hukumar nan da ke ba da agajin gaugawa ta jihar wato SEMA ta tabbatar da aukuwar lamarin inda mai magana da yawun hukumar ya tabbatar wa da majiyar tamu aukuwar hakan.
Sai dai kuma jami\’in hulda da jama\’a na hukumar Umar Muhammad ya bayyana cewa kawo yanzu babu wani takamaiman kiyasin barnar da ruwar ya yi ba.