Rabo Haladu Daga Kaduna
MA\’AIKATAR harkokin cikin gidan Saudiyya ta ce wani gini ya ruguje lokacin da ɗan harin ƙunar-baƙin-wake ya tarwatsa kansa a ciki
Ƙasar Saudiyya ta ce ta daƙile wani \”yunƙurin harin ta\’addanci\” da aka so kai wa Masallacin Harami a Makkah – wurin ibada mafi tsarki ga musulmi.
Wani ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa lokacin da dakarun tsaro suka zagaye ginin da yake ciki, in ji ma\’aikatar harkokin cikin gida.
Ginin ya ruguje, inda ya jikkata mutum 11 ciki har da \’yan sanda. Jami\’ai sun ce an kuma kama wasu \’yan ta-da-ƙayar-baya guda biyar da ake zargi.
Miliyoyin al\’ummar musulmi ne daga faɗin duniya ke taruwa a Makkah don aikin Umrah a ƙarshen azumin watan Ramadan da sauran watanni 11.
Jami\’an Saudiyya ba su fitar da ƙarin bayani a kan harin ta\’addancin da suka daƙile ba.
A shekarun baya-bayan nan, ƙasar Saudiyya ta fuskanci jerin munanan hare-hare, ƙungiyar IS mai iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin kai da dama a cikinsu.
Akasarin hare-haren, ana kai su ne kan tsirarun mabiya ɗariƙar Shi\’a na ƙasar da kuma dakarun tsaro.
A watan Yulin shekara ta 2016, an kashe jami\’in tsaro huɗu a wani harin ƙunar-baƙin-wake da aka kai kusa da Masallacin Annabi a Madina.
Saudiyya dai na cikin rubdugun mayaƙan da ke gwabza faɗa da ƙungiyar IS da sauran wasu \’yan bindiga masu iƙirarin jihadi a ƙarƙkashin jagorancin Amurka a Siriya da Iraki