SAUYA SUNAN JAMI\’AR NORTHWEST – Ko Gwamnatin Kano Ta Kyauta?

0
806
Daga Muhammad Sulaiman Abdullahi
BAYAN rasuwar mai girma Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda Allah ya yi wa rasuwa a wani asibiti a kasar Masar a garin Alkahira, a ranar Litinin din da ta gabata, wato 3 ga watan 7 na 2017, al\’ummar jihar Kano sun shiga jimami da alhini wanda aka dade ba a shiga irinsa ba. Bayan an kammala jana\’izarsa, kuma al\’ummomi da dama suna ta fadar albarkacin bakinsu. Har zuwa yau ban ji wani wanda ya fadi wani abin assha daga bangaren marigayi mai girma Danmasanin Kano, da fatan Allah ya kai rahama zuwa gare shi, muna addu\’ar Allah ya sa abubuwan da ake fada game da shi na alheri, su kai gare shi, inda ya yi kura-kurai kuma, Allah ya yafe masa.
Kwatsam! Bayan rasuwarsa da kwana biyu, sai maganganu suka yi yawa daga bangaren dandalolin sadarwa kamar na facebook da Wat\’s\’af, inda aka dinga yada jita-jitar cewa wai an sauya suna Jami\’ar Northwest, wanda mai girma tsohon Gwamnan Kano ya assasa. Wannan abu ya dauki hankalin mutane, ta yadda aka dinga yada maganar, alhalin kuwa gwamnati ba ta yi hakan ba.
Maitama Sule ya cancanci dukkanin wani suna da za a sa nasa a ko\’ina ne. Domin ya yi abin da da yawa daga cikin al\’umma ba su yi. Don haka duk inda aka sa sunansa, wannan abu ya yi. Abin da bai dace ba shi ne, a sa sunansa a inda siyasa za ta iya taka rawa, kuma hakan ba zai yi wa al\’umma dadi ba.
Wasu daga cikin \’yan\’uwa ba su fahimci dalilan da suka sa muke sukar lamirin wannan lamari ba. Ba wai ana yin hakan domin mai girma gwamna Ganduje ko sanata Kwankwaso ba ne. Mu bayaninmu ya wuce nan. Ai marigayi Maitama ya wuce nan. Ko Kano aka sauya wa suna aka sa sunansa, ba a yi laifi ba!
Bari mu yi gwari-gwari. An taba yin irin haka a Kano. Shekarau ya sanya wa jami\’ar KUST jami\’a sunan Alhaji Dantata, da Kwankwaso ya dawo, ya sauya wannan sunan, kuma haka aka yarda. Yanzu kana ganin hakan ba zai kawo tangarda ba. Shugaba Jonathan ma ya taba yin haka, a Ikko, kuma sunan Abiola ya sa wa jami\’ar Ikko, mutane suka turje suka ki yarda. Ala tilas ya janye. Don haka, su \’yan siyasa, siyasarsu ce a gabansu fiye da komai. Ya kamata a ce sun yi abin ta hanyar shawara da bi a hankali. Mutunci da kimar Danmasani ta wuce nan. Kuma ya kamata a ce an tsaya an yi dogon tunani, ba wai a dinga yin abu yadda aka ga dama ba.
GA MAFITA
Ya kamata idan gwamnatoci za su yi haka, to majalisa ta yi doka. Dokar ta tabbatar da a daina sauya sunayen wurare musamman jami\’o\’i, domin idan an yi haka za a sami sauki ta yadda wani Gwamnan ba zai zo ya sake sauyawa ba. Jami\’a ba kasuwa ba ce, ba asibiti ba ce kuma ba gada ba ce balle wani gini na sharholiya. Tana da Farfesoshi da Daktoci da manyan ma\’aikata iri-iri. Bai kamata a dinga sa siyasa a cikin harkokinta. Akwai takardu da mujallu da makaloli da sakamakon jarrabawa da abubuwa da dama, wasu ma galibi suna kan yanar gizo. Duk fa an sauya wa abubuwa alkibla ba tare da wani babban tunani ba.
Za ta iya yiwuwa wannan gwamnati ta yi haka ne don siyasa ko kuma don kishin kasa. Idan don siyasa ne, to gaskiya ba a kyauta ba kuma ya kamata a guji gaba. Sannan kuma akwai gine-gine da yawa sababbi wadanda, da su aka sa wa sunan da ba za ka ji kowa ya yi magana ba. Ga sabuwar gadar Bukavo. Ga asibitin Giginyu da Zoo Road. Ga gadar Sabon gari. Ga sabuwar gadar hanyar Madobi da ake cewa ba kamar ta a duk Afirka. Ga abubuwa nan da yawa.
Idan kuma don kishin kasa aka yi, to muna fatar Allah ya sa kar wani Gwamnan ya zo ya sake sauyawa, domin an taba yin hakan kamar yadda na ambata, kuma abin ya zo bai yi dadi ba.
Allah ya jikan Danmasani ya taimaki shugabanninmu.
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami\’ar Bayero,
Kano.
08065846225

muhammadunfagge@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here