An Kama Masu Hada Jabun Takin Zamani A Kano

0
839

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

RUNDUNAR \’yan sandan Nijeriya sun yi nasarar kame wadansu masu cutar da al\’umma ta hanyar hada jabun takin zamani suna sayar wa manoma
Rundunar \’yan sandan ta bakin kakakin ta Magaji Musa Majiya ya shaida wa manema labarai cewa sun samu wannan nasarar ne sakamakon bayyana wa rundunar irin yadda macutan suke gudanar da ayyukansu, wanda tun lokacin da aka shaida masu abin da ke gudana nan da nan suka shiga kasuwar Singa suka kuma yi nasarar cafke wadannan mutane bata-gari.
\”Hakika wadannan \’yan kishin kasa da suka sanar wa rundunar \’yan sanda ta Kano sun yi daidai, mun kuma je inda muka tarar macutan sun hada takin zamani har buhuna dari biyar suna kuma yin hakan ne ta hanyar samun takin gwamnatin tarayya mai kyau sai a zazzage buhu daya inda kuma za su fitar da a kalla buhunan takin zamani guda biyar wanda duk kasa kawai suke sayar wa da jama\’a musamman manoma\”.
Majiya, ya ci gaba da cewa suna zuwa ne su yi jabun buhunan takin gwamnatin har da tambarin Nijeriya da komai da yake a jikin buhu mai kyau don kawai manoma su dauka taki ne mai kyau.
Babu wanda zai shiga tsakaninmu da wadannan mutane sai mun gurfanar da su gaban kuliya da duk mai daure masu gindi baki daya.
Kwamishinan ma\’aikatar gona na Jihar Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa hakika duk wanda aka samu da irin wannan yana cutar da jama\’a sai ya fuskanci hukuncin shari\’a.
\”Suna hada jabun takin ne ta yadda ko ka je ka yi amfani da takin a gonarka zai kone maka shuka ta bushe ko kuma ka tarar tamkar ka zuba kasa kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here