DANGOTE ZAI ZUBA KUDI KIMANIN DALA BILIYAN $4.6 A HARKAR NOMA

0
944

Daga Usman Nasidi

KAMFANIN Dangote da aka sani da Dangote Group, wanda Aliko Dangote mafi arzikin mutum a Afirka ke jagoranta sun ba da sanarwar cewa za su zuba makudan kudi kimanin Dala Biliyan $3.8 don noman sukari da shinkafa da kuma Dala Miliyan $800 wa harkar kiwo a nan da shekaru uku masu zuwa don tallafin magance karancin Dala a kasar Najeriya.
Majiyarmu ta kalato cewa Edwin Devakumar, Daraktan kamfanin na reshen Jihar Legas ya ba da sanarwar cewa kokarinsu shi ne ganin sun kara Miliyan daya a kan shinkafa don yawan bukatar sukari da ake yi ton miliyan 1.5 a shekarar 2020.
Kamfanin kuma na cikin tsare-tsaren tanadar shanu 50,000 don samar da nono kimanin lita miliyan 500 a shekarar 2019.
Devakumar ya kara da cewa, rashin musayar kaya tsakanin kasar Najeriya da kasashen waje na haifar da rashin kudi a matattarar mutane kuma yana sanya nauyi ga harkar noma gun yunkurin biyan bashin da ke iya hawa kan gwamnatin kasa. Dole ce take sa mu sayo sukari danye daga waje a tsadance tare da kashe makudan kudi.
Kamfanin simintin Dangote, wanda yake shi ne mafi girma, su kansu suna yunkurin shiga harkar noma a yayin da gwamnatin kasar ke kokarin canza alkiblarta daga amfani da man fetur wanda shi ne kusan kaso 90 na madogarar kasar a harkar canji tsakanin Najeriya da kasashen waje.
Babban kamfanin ya samar da reshen Shinkafa (Dangote Rice Ltd) kuma yana kokarin noma hektar kasa kimanin 350,000 hectares (864,850 acres) na kasa don bunkasa noman rake, sannan hekta 200,000 hectares wa bunkasa noman shinkafa.
Kamfanin dai na Dangote suna cikin tsare-tsare da shirye-shirye a kan harkar noma ta bangarori masu yawa kamar; waken suya,masara,kwawar mai da sauransu tare da samar da takin zamani don ci gaban hakan.
A lissafin duniya na masu arziki, kamfanin Aliko Dangote, dan shekara 60, ya kai darajar kudi Dala Biliyan $12.1 a yayin da yake cikin kamfanunnuka 100 mafi shahara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here