RUNDUNAR SAMAR DA ZAMAN LAFIYA TA YI GARGADIN RUSHE GIDAJEN ‘YAN SARA-SUKA DA KE JOS  

  0
  989
  Isah Ahmed, Jos
   
  GANIN irin yadda ayyukan ta’addancin ‘yan sara suka ya  addabi al’ummar garin Jos babban birnin jihar Filato. Kwamandar  rundunar tsaro mai aikin samar da zaman lafiya a jihar Filato  Manjo Janar Rogers Nicholas ya yi gargadin cewa rundunarsa, za ta  rushe duk wani  gida da aka sami ‘yan sara-suka a garin na Jos. Kwamandan ya yi  wannan gargadin ne a wajen wani taro da ya yi da shugabannin addinai da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki na garin Jos, kan yadda za a magance ayyukan ta’addancin na ‘yan sara suka a garin na Jos.
  Ya ce daukar wannan mataki da rundunarsa tayi ya zama wajibi a gareta ganin irin yadda wadannan ‘yan sara suka suka addabi jama’a a garin na Jos.
  Ya ce bisa binciken tsaro da aka gudanar an gano cewa mafiya yawa da cikin wadannan kungiyoyi ‘yan sara suka, da suka addabi jama’a a garin na Jos, ba ‘yan Nijeriya ba ne.
   ‘’Daga yanzu idan jami’anmu suka biyo irin wadannan ‘yan sara suka, suka shiga wani gida idan har ba a fito mana da su ba, nan take zamu rushe wannan gida. Domin ba za mu amince wadannan ‘yan sara suka, su ci gaba da irin wannan ta’addanci da suke aikatawa ba. Kuma ba za mu amince wadannan ‘yan sara suka, su sake mayar da mu baya ba, kan zaman lafiyar da aka samu a jihar nan’’.
  Kwamandan ya yi bayanin cewa  babban kalubalen da suke fuskanta kan wannan aiki, shi ne idan sun kama irin wadannan ‘yan sara suka, suka mika wa ‘yan sanda aka gurfanar da su a gaban kotu, daga bisani akan bayar da belinsu.
  Ya ce waxannan ‘yan sara suka, suna daukar miyagun makamai tare da aikata miyagun ayyuka kamar far wa jama’a da sace sacen jama’a da aikata fade. Ya ce sun hada hannu da sauran jami’an tsaron jihar don magance ayyukan wadannan ‘yan sara suka.
  Kwamandan ya gargadi iyaye yara da sauran shugabannin al’umma  da ke garin na Jos, kan su dauki matakan ganin sun tura yaransu zuwa makarantu maimakon barinsu suna yawace-yawace.
  Tun da farko a wajen taron shugabannin addini da sauran shugabannin masu ruwa da tsaki a garin na Jos,  sun goyi bayan rundunar kan daukar wannan mataki, na  kama wadannan ‘yan sara suka. Don ganin an magance irin ayyukan ta’addancin da suke aikatawa a garin.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here