WANI MUTUMI YA MUTU A CIKIN JIRGIN EMIRATES A JIHAR LEGAS

0
783
WANI Mutumi dan Najeriya fasinjan jirgin saman Emirates ya mutu ne a jirgin a ranar Laraba da ta wuce da isar su filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.
Bincike da bibitar bayanai sun nuna cewa sunan wanda ya mutun a jirgin saman mai Lamba EK783 (DX) Olusola Dada wanda ke da lambar fasfot A04501199.
Mai magana da yawun filin jirgin saman na \’yan sanda,Joseph Alabi ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a ranar Alhamis.
Mista. Alabi, Mataimakis sufurtanda na \’yan sanda ya ce sanarwar ta iso gare su ne bayan likitoci sun tabbatar da mutuwar fasinjan.
Mamacin da ya taso tun daga kasar Amurka tare da matarsa ya mutu ne tun kimanin karfe 3.55 na yamma a yayin isarsu.
Majiyarnu ta kalato cewa likitoci sunyi iya bakin kokarinsu gun ganin sun ceto ransa, amma basu samu yin hakanba, sun sanar da mutuwar tasa ne a dai dai karfe 5.34 p.m.
wasu karin bayanai sun nuna cewa mamacin ya kasance zababben Gwamna ne na yankin na \’Babbar Kungiyar Lions Club International, District 404 A1\’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here