ZABABBUN TAMBAYOYI KAN AIKIN HAJJI DA UMRA DA ZIYARA
Daga DSP Imam Ahmad Adam Kutubi
Zone 7 Police Headquaters Wuse Zone 3, Abuja
08036095723
WAJIBCIN AIKIN HAJJI SAU DAYA A SHEKARA
TAMBAYA: Shin wajibi ne ga mai iko duk shekara sai ya yi aikin hajji? Ko kuwa sau daya ne yake wajibi?
AMSA: Ba dola ba ne sai an yi duk shekara, na wajibi sau daya ne a rayuwa. Koda kuwa mutum yana da iko, baya zama dole a kansa, kamar yadda ya zo a cikin Hadisai da dama cewa Manzon Allah S.A.W ya tara mutane ya yi musu Huduba ya kwadaitar da su kan aikin Hajji, sai wani Sahabi mai suna Akara’u dan Habis ya mike ya ce: ya Ma’aikin Allah shin duk shekara sai an yi? Sai ya ce: (a’a da na ce e da sai ya zama wajibi, saudaya ake aikin Hajji).1
*****
WANDA YA ZO DON YIN UMARA, HAJJIN WANNAN SHEKARA BA TA WAJABA A KANSA BA
TAMBAYA: Wanda ya zo don yin Umara shin dole ne sai ya yi Hajjin wannan shekara? Saboda muna jin mutane suna fadar hakan, shin gaske ne?
AMSA: Wannan kuskure ne, babu wanda ya fadi hakan cikin malaman Musluunci.
*****
YIN HARAMAR YARO DON YIN HAJJI KO UMARA
TAMBAYA: Shin ya halatta ga yaran da ba su kai shekaru bakwai ba su yi dawafi tare da mahaifansu?
AMSA: Ya halatta su yi haramar Hajji ko ta Umara, ko da ba su kai shekaru bakwai ba, kamar yadda ya zo a kissar matar nan Khas’imiyah wacce ta dauko karamin yaro da ke cikin shawul ta ce: ya Ma’iakin Allah! Shin wannan zai iya yin Hajji? Ya ce: Kwarai kuwa amma ladar ta ki ce), ta nan aka gane cewa Umarar yaron da bai kai shekaru bakwai ba ta halatta, kuma ya iya yin Hajji da dawafi amma a matsayin nafila.
*****
IDAN MACE ZA TA IYA YIN HAJJI TO YA HAU KANTA
TAMBAYA: Mace ce take da ‘ya‘ya ‘yan shekaru tara zuwa ashirin, kuma tana da miji ya yi Hajji amma ita ba ta yi ba, tana kuma da da balagagge, shin Hajji ta hau kanta?
AMSA: Na’am idan tana da iko, tana da dukiya za ta iya zuwa Makka ta dawo ba tare da bashi ba, ba tare da rokon mutane ba, Hajji ya wajaba akanta a kowane hali, danta zai iyi tafiya da ita hajjin, amma idan talaka ce hajji bai hau kanta ba, saboda Allah (S.W.T) yana cewa:
Ma’ana: (Allah ya wajabta aikin Hajja kan mutane ga wanda ya samu iko) Surar Ali Imran: 97, Iko shi ne Guzuri da abin hawa, a zamanin yanzu kuma guziri da kudin jirgi, idan kuma ba ta da komai to Allah ba ya dora wa mutum abin da ba zai iya ba, wannan ana magana ne kan Hajjin farillah.
*****
SHIN WAJIBI NE MIJI SAI YA YI HAJJI DA MATARSA?
TAMBAYA: Shin wajibi ne miji sai ya yi Hajji ko Umara da matarsa?
AMASA: Ya kamata ya yi Hajji da ita, ya kyautata mata amma babu batun dole, ba dole ne sai ya yi Hajji ko Umara da ita ba, kawai dai kyautatawa ce daga gare shi, ya kamata ya yi hakan, amma idan bai yi ba, ba shi da wani laifi.
****
YIN HAJJI DA DUKIYAR HARAMUN
TAMBAYA: Mene ne hukuncin wanda ya yi Hajji ko Umara ta hanyar kudin giya, saboda ba shi da wasu?
AMSA: Abu ne sananne cewa Annabi S.A.W. ya yi bayani kan wannan tambayar inda yake cewa:
Ma’ana: (Hakika Allah idan ya haramta abu sai ya haramta cin Kudinsa) 2 Shin giya haramun ce? Amsar ita ce ‘e’ babu tantama cewar haramun ce, sai mu ce matukar dai haramun ce, to kudinta ma haramun ne saboda Annabi S.A.W yana cewa “Allah idan ya haramta abu sai ya haramta Kudinsa” don haka cin kudin giya ko amfani da su bai halatta ba, kamar yadda mushe yake haram bai halatta a yi amfani da nama ko kitsansa ba.
A TAKAICE: Cin kudin giya haramun ne, idan hakan ta faru dole ka tuba ka yi istigfari, idan ka yi tuba na gaskiya ana sa ran Allah zai yi maka afuwa ya gafarta maka, shi kuwa tuba yana da sharuddai uku:
– Na farko: Yin nadama kan abin da aka aikata
– Na biyu: Ka kudurce cewa ba za ka kuma ba.
– Na uku: Ka yi bakin ciki kan abin da ka aikata, ka kuma nisanci aikata makamantan sa.
****
WANDA YAKE DA IKO BAI YI HAJJIN FARILLA BA WANI BA ZAI YI MASA BA?
TAMBAYA: Ni ma’aikacin gwamnati ne, amma tsawon shekaru ashirin ban yi aikin Hajji ba, yanzu kuma aiki ya yi min yawa ba zai yiwu in bar wajen aikina ba, shin zan iya wakilta wani ya yi min aikin Hajji?
AMSA:Matukar dai kana da karfi kuma za ka iya yin aikin Hajji, kamata ya yi ka nemi izini wajen shugabanninka, ka fada musu cewa har yanzu ba ka yi Hajjin wajibi ba, babu shakka za su ba ka dama sai su sa wani ya kula da aikinka, saboda Hajjin wajibi dole ce ga mai iko, don haka bai halatta ka aika wani ya yi maka ba, bayan kana da ikon yi.
****
SAKA WAKILCI A AIKIN HAJJI
TAMBAYA: Ina daukar nauyin hajjin mahaifana, daga garin Riyad duk shekara ina kashe sama da Riyal dubu uku don a yi musu Hajji, Sai na sami wani mutumin a Makka zai yi musu Hajji da Umra a Riyal Dubu Biyu, shin hakan ya halatta kuma wanne ne ya fi?
AMSA: Idan a Riyad din ka sami mutumin kirki mai tsoron Allah da zai yi cikakkiyar Hajji, ina gani kamar zai fi saboda abin da aka fi bukata shi ne mutumin kirki nagari, ya karbi abin da yake ganin zai ishe shi har ya gama aikin hajjinsa, ina ganin babu laifi, kuma Allah zai karba ya baka lada.
*****
SHARADI NE WANDA ZA A WAKILTA YA ZAMA YA FARA YIN TASA HAJJIN TUKUNNA
TAMBAYA: Na yi aikin Hajjina kafin in balaga, bayan kuma na balaga sai na yi wa wasu Hajji har sau biyu a jere, shin Hajjin da na yi musu ta yi, tare da cewa na yi tawa ne kafin in balaga?
AMSA: Hajjinka da ka yi kafin ka balaga wannan nafila ce, wacce kuma bayan ka Balaga ka yi wa mutum biyu to, ba ta yi ba, sai dai ta sun ta farko ta zama taka kamar yadda yake a Mazahabin Hanbaliyya da wasunsu cewa: Idan mutum ya yi wa wani Hajji kafin ya yi wa kansa, to tana mazaunin tasa; ko da kuwa ya yi niyyar yi wa wancan din, don haka ta farkon taka ce kai kanka, ta biyu kuma ta wanda ka yi niyar yi wa ce. Ya zo a kissar Sahabin nan mai suna (Shubramata) cewa:((Annabi S.A.W ya ji wani mutum yana cewa (Amsawarka wannan Hajjin Shubramarata ce) Annabi S.A.W ya ce wane ne Shubramata? Ya ce dan’uwana ne, “Annabi S.A.W ya ce: Shin kai ka yi wa kanka Hajjin ne? Ya ce : a’a, «Annabi S.A.W.» ya ce : ((ka fara yi wa kanka Hajjin tukuna sannan ka yi wa Shubramata)), tare da cewa sa’adda zai yi harama ya yi ne da niyyar dan’uwansa amma Annabi S.A.W. bai ce ya sake harama ba, sai ya sa shi kawai ya canja niyya, malamai suka ce wannan yana nuna idan mutum ya yi wa wani hajji bayan shi bai yi ba, to tasa ce.
****
YI WA MAHAIFIYA HAJJI IDAN BA ZA TA IYA BA
TAMBAYA : Wani mai tambaya yana cewa : yana da mahaifiya tana so ta yi Hajji sai dai ta yi nisa da yawa, ita kuma ba za ta iya hawa mota ba, shin ya halatta ya yi mata Hajji?
AMSA: Idan ba za ta iya hawa jirgi ko mota ba, babu laifi ka yi mata Hajji in ta yarda, amma idan za ta iya zuwa to dole ne sai ta yi Hajjin farilla da kanta, bai halatta a yi mata Hajjin farilla ba matukar za ta iya yi, sai dai in ba za ta iya ba.
*****
YI WA MACE HAJJI BAYAN TANA RAYE
TAMBAYA:Ni mutumin Siriya ne na yi hajji sau biyu, mahaifiyata ma ta yi dan’uwana kuma ya yi wa mahaifimmu. Ina da ‘ya‘ya bakwai duk yara, matata kuma tana gida ba za ta iya barin yara su kadai a gida ba, shin zan iya yi mata Hajji?
AMSA: Idan tana da karfin da za ta iya, kuma Hajjin farilla ce, to dole ta yi da kanta, amma idan ta nafila ce to babu laifi in ta yi izini, ba a yi wa mutum Hajjin farilla matukar yana da karfi da iko kuma zai iya yi, idan yara sun girma dole ta je ta yi ko kuma a nemo wacce za ta zauna a gidan ta kula da yara.
****
TAMBAYA: Idan na yi niyyar wakiltar wani a Hajji, ni kuma a niyyata so nake na yi hajji da Umara, shin dole ne sai mun yi da shi cewa Hajji da Umara, ko kuwa in na ce masa hajji kawai ya isa?
AMSA: Idan ka wakilta wani kan hajji ya kamata ka fada masa cewa Hajji da Umara kake so, idan ba ka fada masa ba Hajji ce kawai a kansa, saboda Umara aiki ne mai zaman kan sa da niyyarta, Hajji ma haka, shi iyaka abin da kuka yi da shi kawai zai yi maka.
****
IDAN MUTUM YA YI WA WANI HAJJI SHIN SHI MA YANA DA LADA?
TAMBAYA: idan aka wakilta mutum ya yi wa wani Hajji aka biya shi, shin Allah zai bai wa wanda aka wakilta din lada?
AMSA:Bai kamata ka karbi lada don za ka yi wa wani Hajji ba, sai dai idan kai mabukaci ne, ba kamar yadda mafi yawan mutane suke yi suna mayar da ita kamar hanyar neman kudi, hakan bai kamata ba, abin da ya dace shi ne ya zamto kai manufarka ita ce kana son zuwa Makka amma ba ka da dama, to a nan idan ka sami wanda zai biyaka, ka yi masa babu laifi ka karbi abin da zai isheka ka je Makka ka yi dawafi, idan ka yi masa Hajjinsa ragowar lokutan naka ne sai ka yi sallolinka na farillah da na nafila, ladar taka ce, ka yi dawafin nafila ladar taka ce ka yi addu’oi, abin da kawai yake na wanda ya biya ka shi ne dawafin ifada da Safa da Marwa da tsayuwar Arfa da jifa da kwanan Mina, amma duk sauran ayyukan da ba sa cikin ayyukan Hajji to ladarsu taka ce.
Za Mu Ci Gaba