Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
MAI alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa\’ad Abubakar ya karyata jita-jitar da ake yadawa a wasu kafafen labarai cewa wai an kirkiri shirin karantar da ilimin addini ne domin a musuluntar da kiristoci.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a garin Bauci wajen taron harkokin yada da\’awa.
Inda ya tabbatar wa da duniya cewa hakika wannan batu ba gaskiya ba ne don haka ya zama wajibi ga kowa a san haka
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron Gwamnan Jihar Bauci ya yi kira ne ga daukacin malamai da dukkan makarantu da su tashi tsaye wajen koyar da ilimin tarbiyya.
Ya kuma bayyana godiya ga majalisar da\’awar kan irin yadda ta zabi jihar domin gudanar da wannan taron na bana.