Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GWAMNATIN Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i ta bayyana cewa haramun ne safara, yanka, ci da mu\’amala da naman jakuna a fadin jihar.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta bayar a kafafen yada labarai inda ake ta sanarwa cewa duk wanda aka samu da daya daga cikin wadannan abubuwa babu ko shakka haramun ne kuma duk wanda aka samu ya kuka da kansa.
Kamar dai yadda aka sani safara,yanka tare da cin naman jakuna na neman zama ruwan dare a duk fadin Nijeriya baki daya.
Bisa ga duba da irin yadda mu\’amala ke neman gagarar kundila musamman yadda wasu daga wasu kasashen ketare ke safarar jakuna zuwa kasar su ya sa dole gwamnatin ta dauki mataki
Tsawon shekarun da suka gabata ana samun wadansu mutanen wata kasa na shigowa Nijeriya suna sayen jaki su fede domin daukar fatar zuwa kasar su.
Ana kuma samun zarge-zargen cewa wasu na yanka jakuna suna sayar wa jama\’a kan rashin sani, amma a wani yanki na Nijeriya har wuraren yankan jakuna suke da su.
Don haka gwamnatin Kaduna ke kira ga jama\’a da kada kowa ya sake a same shi da wannan aikin da ya zama laifi a Jihar.