Daga Usman Nasidi
YAWAN Hausawa a Legas kam musamman a garin Agege ya isa a ce sun kai matsayin su iya tsayar da dan takara nasu kuma su samu ikon aiwatar da hakan matukar zabe zai kasance a kan adalci, wannan tunanin ya kasance dadadde ne da ke kai kawowa a kwakwale da zukatan masarauta, jagorori, da maluman garin Agege.
A yunkurin tabbatar da wannan tunani na mazauna garin, an yi ta sanya ran kungiyoyin siyasa, matasa da jagorori su hadu don tabbatar da hakan da dadewa, amma hakan bai yiwu ba sai wannan karon da Allah ya kaddara guguwar canji ta farkar da matasan garin suka nuna lokaci ya yi da ya kamata a zartar da hakan.
Sanannen abu ne cewa \’yan garin Agege na farko sun shahara da harkar goro, a yayin da \’yan bana bakwai suka shahara da harkar canji, amma duk da haka Agege na da \’yan boko masu digiri, da digirgir da ke iya kaiwa kimanin mutane 100.
Majiyarmu ta nakalto cewa jam\’iyyar siyasar PDP ta amince da tsayar da dan Arewan a matsayin dan takararta a karamar hukumar Agege mai suna Auwal Tahir Maude (Adeniyi) ATM sakamakon kasancewarsa dan boko Injiniya mai matakin digiri na biyu,wato Masters, dan kasuwa mai hangen nesa, kuma mai mu\’amalar sarrafa yarurruka uku.
Injiniya Auwal Tahir Maude, wanda aka fi sani da ATM, ya samu cikakken goyon baya daga Hausawa mazauna garin na Agege kama daga, masarauta,malamai, matasa, \’yan kasuwa, kungiyoyin addini da ‘yan kabilar Yarbawa.
A jawabinsa da yake yi wa jami\’in labaranmu na NAIJ.com , dan takarar ya bayyana cewa daukacin ‘yan arewa mazauna wannan yanki na taka rawar gani wajen ba da cikakken hadin kai musamman wajen harkokin siyasa da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewa.
Injiniya Auwal, ya kara da cewa akwai ‘yan kabilar Yarbawa da dama da ke mara masa baya domin a cewarsa zaman tare da Hausawa ‘yan arewa ke yi da ‘yan kabilar ta Yarbawa ya sa sun zama tamkar tsintsiya madaurin ki daya.
Manyan masu unguwannin Yarbawa da shahararru cikin mazauna yankin sun bayyana cewa suna daga cikin masu mara wa Bahaushe dan arewa baya domin kasancewar sa haifaffen karamar hukumar ne kuma kasancewarsa yana iya sarrafa yare da harsuna uku wato Yarbanci da Hausa da kuma Turanci, wanda haka zai kawar da matsalar cudanya tsakanin su.