ZABEN JIHAR LEGAS: LAUYAN APC YA KOKA A KAN ZA A HALLAKA SHI

    0
    698
    Daga Usman Nasidi
    BABBAN lauyan jam’iyyar \’All Progressive Congress\’ APC na kasa Dokta Muiz Banire (SAN), ya ce rayuwarsa na cikin hatsari.
    A wata takardar bayani da Banire ya sa hannu, ya ce wani tsohon shugaban karamar hukuma da wani kwamishina na yanzu a Jihar Legas suna yi shirin yin wani taro a ranar Talata don shirya yadda za a hallaka shi.
    Ya ce suna so su ga bayan shi ne saboda ka’idarsa na yin abin da ya dace a jam’iyyar.
    Zaben kananan hukumomin jihar Legas: \’Rayuwana na cikin hatsari\’-Lauyan APC Banire\’.
    Reshen jam’iyyar na jihar Legas suna zargin Banire da hana zaben fitar da gwani a karamar hukuman Obi-Olowo wanda zai tsaya a zaben kananan hukumomi da za a yi nan gaba.
    Banire ya musanta shiga lamuran kotu,ya kara da cewa ya yi kokarin kare jam\’iyyar ne kawai a kotu a matsayin shi na lauyan jam’iyya.
    A shekaranjiya Litinin Banire yake ce wa ya ji labarin wani tsohon shugaban karamar hukuma Seye Oladejo, da kuma kwamishinan ayyuka na mussamman a jihar Legas suna hada wani taro don su ga sun hana mutane cin moriyar dimokuradiyya kuma taron zai gabata ranar Litinin 18 ga watan Yuli na 2017.
    Sun hada wannan taron ne don bata ni saboda su samu nasarar dora wadanda suke so su tsaya takara ba zabin jama\’a ba.
    Ina amfani da wannan dama ne in ja musu kunne, barazanar da suke yi wa rayuwata, ba zai hana ni yin aiki na ba na hana danniya da dora wa mutane dan takarar da ba sa so.
    Ina jan hankalin magoya bayan jam’yyar APC da kada su bari a ruda su har a dora musu dan takarar da ba sa so.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here