AKALLA MUTANE 33 SUKA MUTU A WANI SABON RIKICIN KUDANCIN KADUNA

2
708
Daga Usman Nasidi
AKALLA mutane 33 ne aka halaka a wani sabon rikici da ya kunno kai tsakanin Fulani da ‘yan kauyukan Kajuru.
Kwamishinan \’yan sandan jihar Kaduna ya ce lamarin ta fara a lokacin da wasu ‘yan kauyen suka kai farmaki ga wani Bafulltani da mahifinsa.
Hukumar ‘yan sanda ta yi alkawarin kama da kuma gurfanar da duk wadanda ke da alhakin haddasa rikicin.
Hukumar \’yan sanda ta ce tun daga ranar Laraba, 19 ga watan Yuli cewa aka fara samun kwanciyar hankula a kauyuka a karamar hukumar Kajuru da ke kudancin jihar Kaduna, inda mutane 33 suka mutu a wani sabon rikici da ya barke tsakanin ‘yan hasalin kauyen da kuma Fulani makiyaya.
Fulani makiyaya 27 mazaunar yankin ne mutanen kauyukan suka kashe a wata harin ramuwar gayya, yayin da kuma mutane 6 suka mutu a tsakanin ‘yan hasalin kauyukan kamar yanda hukumar \’yan sanda a jihar ta sanar a Kaduna.
Kwamishinan \’yan sanda a jihar, Mista Agyole Abeh a wani taron manema labarai yana mai cewa, lamarin ta fara a ranar 11 ga watan Yuli a lokacin da wasu ‘yan kyauyen suka kai farmaki ga wani yaro Bafulltani da mahaifinsa.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa \’yan sanda za su kama da kuma gurfanar da duk wadanda ke da alhakin wannan danyen aiki.

2 COMMENTS

  1. A gaskiya bai kamata ace ana neman a zauna lafiya amma kuma wasu sutashi su kaiwa wasu farmaki ba,haka baiyi dai daiba. dan haka yana da kyau Hukuma ta bincika ta kuma gurfanar da duk wanda yace da laifi,dan mu zaman lafiya mukeso a kasarmu.

  2. A gaskiya bai kamata ace ana neman a zauna lafiya amma kuma wasu sutashi su kaiwa wasu farmaki ba,haka baiyi dai daiba. dan haka yana da kyau Hukuma ta bincika ta kuma gurfanar da duk wanda yace da laifi,dan mu zaman lafiya mukeso a kasarmu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here