Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN kungiyar masu shayi ta kasa Alhaji Shu’aibu Abubakar ya
bayyana cewa ya bude wurin sayar da shayi irin na zamani ne, don dada
inganta wannan sana’a. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake
jawabi a wajen walimar bude wajen sayar da shayi irin na zamani da ya
yi a garin Jos.
Ya ce mun bude wannan wajen sayar da shayi irin na zamani ne, domin
wurin shayi wurin cin abinci ne da ya kamata a inganta shi fiye da
kowanne irin wurin sana’a. Domin wuri ne na kiwon lafiya.
Ya ce mun kawata wannan waje mun sanya masa dukkan abin da ya kamata
mu sanya, mun yi kamar yadda ake wuraren sayar da shayi a kasar
Saudiyya da sauran manyan kasashen duniya.
Ya yi kira ga masu shayi na Nijeriya, su bude irin wadannan wuraren
sayar da shayi irin na zamani domin inganta wannan sana’a tare da
kwantarwa da abokan huldarsu hankali.
Shi ma a nasa jawabin babban jami’in ‘yan sanda na shiyar Unguwar Rogo
dake garin Jos Mansur Ahmed ya nuna jin dadinsa da bude wannan waje.
Ya ce babu shakka an yi kokari wajen gyara wannan waje. Ya yi fatar
sauran masu sana’ar shayi zasu koyi da wannan abu.
Daga nan ya yi kira ga masu wannan sana’a su bai wa jami’an ‘yan
sanda hadin kai da goyan baya ta hanyar basu labaran masu aikata
miyagun abubuwa. Ya ce irin wadannan labarai za su taimaka masu wajen
gudanar da ayyukansu.
Manyan mutane da sauran kungiyoyi da dama ne suka halarci wajen wannan
walima ta bude wannan waje na sayar da shayi irin na zamani a garin na
Jos.